An yi zanga-zangar sanya gajeran wando a Azerbaijan
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da zanga-zangar neman damar sanya gajeran wando a birnin Baku na kasar Azerbaijan, kamar yadda shafin Intanet na Odu.az news ya ruwaito.kasar wadda take a nahiyar Turai, tana da jama’a fiye da miliyan tara wadanda galibinsu Musulmi ne. Kodayake, gwamnatin kasar ta kasance wadda ba ruwanta […]
A ranar Lahadin da ta gabata ne aka gudanar da zanga-zangar neman damar sanya gajeran wando a birnin Baku na kasar Azerbaijan, kamar yadda shafin Intanet na Odu.az news ya ruwaito.
kasar wadda take a nahiyar Turai, tana da jama’a fiye da miliyan tara wadanda galibinsu Musulmi ne. Kodayake, gwamnatin kasar ta kasance wadda ba ruwanta da addini kuma jama’ar kasar suna sanya tufafi ne irin na Turawa.
An ruwaito cewa matasa da dama ne suka amsa kiran, inda suke neman a kyale su su rika sanya gajeran wando ba tare da wata tsangwama ba. An dai yi amfani da kafar sada zumunta ta Facebook ne wajen kiran zanga-zangar bayan da wani jagoran wata jam’iyya a kasar ya yi kira da jama’a kan su rika tozarta duk wani ko wata da ya sanya gajeran wando.
Duk da cewa ana samun yanayin zafi a kasar, kuma ’yan kasar sun saba da sanya suturan Turawa, amma mutanen can sun sha nuna rashin gamsuwarsu da hakan.