An zaɓi mace ta farko a matsayin Shugabar Ƙasa a Namibiya
An zaɓi Netumbo Nandi-Ndaitwah, a matsayin mace ta farko da ta zama Shugabar Ƙasa a Namibiya.
An zaɓi Netumbo Nandi-Ndaitwah, a matsayin mace ta farko da ta zama Shugabar Ƙasa a Namibiya.
Nandi-Ndaitwah mai shekaru 72 a duniya, ta kasance Mataimakiyar Shugaban Jam’iyyar SWAPO mai mulki.
- Majalisa ta kafa kwamitin da zai yi nazari kan dokokin gyaran haraji
- Shugaban Korea ta Kudu ya kafa dokar ta ɓaci don hukunta ƴan adawa
An gudanar da zaɓen a ranar 27 ga watan Nuwamba, amma samu jinkiri wajen bayyana sakamakon zaɓen saboda matsalolin na’urorin aiki.
A ranar Talata, Hukumar Zaɓe ta Ƙasar, ta sanar da cewa Nandi-Ndaitwah ta lashe zaɓen da kashi 57 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Ta doke babban abokin hamayyarta Panduleni Itula na jam’iyyar IPC, wanda ya samu kashi 26 na ƙuri’un da aka kaɗa yayin zaɓen.
Jam’iyyar SWAPO ta kuma samu rinjaye a Majalisar Dokokin ƙasar, inda ta lashe kujeru 51 daga cikin 96.
Nandi-Ndaitwah, ta yi alƙawarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta hanyar shimfiɗa ayyukan da za su ciyar da ƙasar gaba.
Sai dai jam’iyyar adawa ta IPC, ta shirya ƙalubalantar sakamakon a kotu, inda ta ayyana zaɓen a matsayin mai cike da kurakurai.
Nasararta na nufin jam’iyyar SWAP za ta ci gaba da mulki na tsawon shekaru 34 tun bayan samun ’yancin ƙasar daga hannun Afrika ta Kudu a shekarar 1990.