An zaɓi Musulmi shugaban gwamnatin Scotland
A shekarar 2011 aka fara zaɓensa ɗan Majalisar Dokokin Sikotland.
A karo na farko, an zaɓi Musulmi ya zama shugaban gwamnatin yankin Scotland dake cikin ƙasar Birtaniya.
Jam’iyyar SNP mai mulki ce ta zaɓi Humza Yousaf a matsayin shugabanta kuma shugaban gwamnatin yankin.
- Saudiyya ta gargadi masu daukar hoto a wuraren ibada
- INEC ta sa ranar kammala zaben Kebbi da Adamawa
Wannan ne dai karo na farko da wata babbar jam’iyya a Haɗaɗɗiyar Daular Burtaniya da Arewacin Ireland ta zaɓi musulmi a matsayin shugaba.
A ranar Talata ne kuma ake sa ran Humza Yousaf mai shekaru 37 zai ɗare kujerar shugabancin Scotland.
Mahaifin Mista Yousaf dai ya yi hijira daga Pakistan zuwa Scotland ne a shekarun 1960 yayin da mahaifiyarsa kuma ƴar asalin Pakistan ce da aka haife ta a Kenya.
A shekarar 2011 aka fara zaɓensa ɗan Majalisar Dokokin Scotland.
Kafin nasara a zaɓen, shugaban gwamnatin ya riƙe muƙamin minista a ma’aikatun sufuri, shari’a, da lafiya.
Bayan da ya yi nasara a zaɓen ya sha alwashin jagorantar Scotland a gwagwarmayar samun ƴancin kai daga Burtaniya.