An zabi Barnabar Banted shugaban APC na Jihar Kaduna

Mista Barnabas Bala Banted ne aka zaba a matsayin shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna a zaben shugabannin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata. An yi zaben ne a Kasuwar Duniya ta Kaduna, inda aka kammala a safiyar Litinin.Da yake bayyana sakamakon zaben ga manema labarai, shugaban kwamitin gudanar da zaben, […]

An zabi Barnabar Banted shugaban APC na Jihar Kaduna
An zabi Barnabar Banted shugaban APC na Jihar Kaduna

Mista Barnabas Bala Banted ne aka zaba a matsayin shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna a zaben shugabannin jam’iyyar da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.
An yi zaben ne a Kasuwar Duniya ta Kaduna, inda aka kammala a safiyar Litinin.
Da yake bayyana sakamakon zaben ga manema labarai, shugaban kwamitin gudanar da zaben, Kanar Mustapha Abdullah (murabus) ya ce an zabi Banted shugaba sannan Alhaji Shu’aibu Idris ne aka zaba mataimakinsa.
Sauran wadanda aka zaba sun hada da Malam Sa’idu Kudan Sakataren Shirye-Shirye da Dokta Katuka Sanaka Jami’in Hulda da Jama’a.
Ya ce, an bi dokokin da aka gindaya wa ’yan takara wajen gudanar da zaben kuma akwai jami’an tsaro da na hukumar zabe da wakilan jam’iyyar ta kasa a wurin zaben.
Ya shawarci wadanda aka zaba da sauran ’yan jam’iyyar su ajiye bambancin da ke a tsakaninsu su hada kai domin jam’iyyar ta cimma nasara.
Wadanda suka tsaya takarar shugabancin jam’iyar sun hada da Sadik Mamman Legas da Mataimaki Tom Maiyashi da Umar Aliyu da Abdullahi Abbas da Ahmadu Coca-Cola da Aliyu Lawal da Mikah Sule da Abubakar Abdullahi da Dokta Hakeem Baba-Ahmed wanda ya janye daga takarar.