An zabi Catherine Samba-Panza shugabar Afirka ta tsakiya

An zabi Magajiyar birnin Bangui Misis Catherine Samba-Panza mai shekara 59, a matsayin Shugabar Rika na Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, inda ta zama mace ta farko da ta rike mukamin a kasar.Ta kada abokin takararta Desire Kolingba a zagaye na biyu na kuri’ar da majalisar riko ta kasar ta kada.Zaben ya zo ne a daidai […]

An zabi Catherine Samba-Panza shugabar Afirka ta tsakiya

An zabi Magajiyar birnin Bangui Misis Catherine Samba-Panza mai shekara 59, a matsayin Shugabar Rika na Jamhuriyyar Afirka ta Tsakiya, inda ta zama mace ta farko da ta rike mukamin a kasar.
Ta kada abokin takararta Desire Kolingba a zagaye na biyu na kuri’ar da majalisar riko ta kasar ta kada.
Zaben ya zo ne a daidai lokacin da ministocin kasashen Turai suka amince a wurin taronsu cewa za su tura sojojinsu zuwa kasar.
Tashin hankali na ci gaba da gudana a kasar, inda aka kashe Musulmi biyu maza aka kone su a babban birnin kasar Bangui a ranar Lahadin da ta gabata.
Kusan mutum miliyan ne aka raba su da muhallinsu, kimanin kashi 20 cikin 100 na jama’ar kasar sakamakon fada a tsakanin Musulmi da Kirista.
A jawabin samun nasara Misis Samba-Panza ta bukaci Kiristoci masu dauke da makamai da ake kira da anti-balaka da mayakan Musulmi na tsohuwar kungiyar Seleka su kawo karshen zubar da jinin da suke yi.
“Ina kira ga ’ya’yana musamman anti-balaka su ajiye makamansu su daina duk wani fada. Haka ma ga mambobin tsohuwar Seleke- baa bin da za su ji tsoro. Ba na son inj ji wasu maganganun kashe-kashe,” kamar yadda kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya ruwaito.