An Zabi El-Rufai Abokin Takarar Tinubu

Kwamitin kamfe na Tinubu ya yi ittifakin dole abokin takararsa ya fito daga Arewa maso Yamma, yanki mafi yawan kuri’i a Najeriya.

An Zabi El-Rufai Abokin Takarar Tinubu

Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu (TSO) a matsayin shugaban kasa a zaben 2023 ya zabi Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin abokin takarar Tinubu.

Bayan wata tattaunawa da TSO ta gudanar a Kaduna, Darakta-Janar na kungiyar, Aminu Sulaiman, ya ce sun yi ittifakin cewa dole abokin takarar Tinubu ya fito daga Arewa maso Yamma, tun da nan ne yanki mafi yawan kuri’i a Najeriya.

“Mun yi amanna mutumin da ya fi dacewa ya zama mataimakin Tinubu shi ne El-Rufai, kuma shi muke so a dauka,” inji Aminu Sulaiman.

A cewarsa, babu wanda ya fi El-Rufai dacewa ya zama mataimakin Tinubu, duba da muhimmancin zabin abokin takara wajen samun nasara a zaben 2023.

Ya bayyana cewa, “El-Rufai na da kwarewa kuma ya rike mukamai a matakin gwamnatin jiha da ta tarayya, sannan a duk mukaman da ya rike ya zama abin buga misali.”

A koyaushe, a cewarsa, El-Rufai mutum ne mai goyon bayan kyawawan tsare-tsaren cigaba kuma ba matsoraci ba ne.

Don haka akwai bukatar samun irin basira da karsashin gwamnan Kadunan a matakin Gwamnatin Tarayya.

Wannan dai na zuwa ne bayan Tinubu da jam’iyyarsa ta APC sun ci gaba da laluben wanda zai zame mishi abokin takara, duk kuwa da cewa sun mika wa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) sunan Masari a matsayin abokin takararsa.

Masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC dai sun ce Masari abokin takara na wucin gadi ne kafin Tinubu ya fitar da ainihin wanda zai mara masa baya.

Kawo yanzu dai Masari da APC ba su ce komai kan neman maye gurbinsa da wani abokin takara ba.

INEC dai ta ce bayyana cewa ba ta san da wani abokin takara na wucin gadi ba, domin babu shi a Dokar Zabe.

Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar Kai, Barista Festus Okoye, ya bayyana cewa muddin jam’iyya ta mika wa Hukumar sunan dan takara, to jam’iyyar ba ta da hurumin sauya shi, sai dai idan shi da kansa ne ya janye ya kuma sanar da hukumar a rubuce tare da gabatar mata da takardar shaidar rantsuwar kotu.

Ko a hakan, wanda aka gabatar a matsayin abokin takara ba zai iya janyewa ba idan ya rage kasa da kwana kasa 90 a gudanar da zabe.

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu