An zabi kare Magajin Gari a Amurka

Wani kare mai suna Wilbur Beast ya lashe zaben zama Magajin Garin birnin Kentucky da ke Amurka bayan da ya samu kuri’a dubu 13 da 143  a zaben da aka gudanar a birnin inda ya samu kuri’u mafi yawa a tarihin zaben a birnin. Birnin Kentucky daya ne daga cikin kananan biranen da ke Arewacin […]

An zabi kare Magajin Gari a Amurka

Wani kare mai suna Wilbur Beast ya lashe zaben zama Magajin Garin birnin Kentucky da ke Amurka bayan da ya samu kuri’a dubu 13 da 143  a zaben da aka gudanar a birnin inda ya samu kuri’u mafi yawa a tarihin zaben a birnin.

Birnin Kentucky daya ne daga cikin kananan biranen da ke Arewacin Amurka inda a ranar Talatar makon jiya karen ya lashe zaben zama Magajin Garin birnin da kuri’u mafiya yawa.

Wilbur Beast,  wanda irin jinsin karnukan kasar Faransa ne ya zama dabba na farko da ya tsaya takara kuma ya lashe zabe a tarihin birnin.

Zaben ya kasance wanda masu kada kuri’a da dama suka fito inda akalla masu kada kuri’a dubu 22 da 985 suka kada kuri’unsu.

Rahotonni sun ce Wilbur Beast ba shi ne kare na farko da ya taba jagorontar birnin ba, domin tun a 1990 ake zabar karnuka a matsayin shugabannin birnin.

Su dai masu kada kuri’un sun fi gamsuwa wajen rubuta sunan karen da suke ganin ya cancanci zama Magajin Garin birnin a takardar kada kuri’a.

Kuma mutanen garin Rabbit Hash sun kasance masu ba da gudunmawar Dalar Amurka daya ga unguwar da suke.

Kare na farko da aka  taba zaba a birnin Rabbit Hash shi ne Goofy Borneman-Calhoun wanda aka rantsar a 1998, don ya yi shugabanci na tsawon shekara hudu.

Sai dai karen bai kammala wa’adinsa ba ya mutu a watan Yulin shekarar 2001, yana da shekara 16.

A bana Wilbur ne zai ci gaba da jan ragamar shugabancin bayan doke Magajin Gari mai ci Brynneth Pawltro wanda aka zaba a shekarar 2017.

Sauran ’yan takarar da suka zama na biyu da na uku sun hada da Jack Rabbit da Poppy wadanda suka samu lambar yabo ta Jakadun Lady Stone ta Rabbit Hash kamar yadda hukumomin birnin suka sanar a shafinsu na Facebook.

Ba a ware neman takarar ba ga tsofaffin karnuka, kowane dan takara na da ’yancin neman kujerar birnin Rabbit Hash a cikin awa daya da aka sanar don fara tantance ’yan takarar neman shugabancin.

Kakakin zababben Magajin Garin birnin wadda mutum ce kuma abokiyar karen mai suna Amy Noland, ta bayyana wa kafar labarai ta Fox News cewa ita da zababben karen sun mika sakon godiyarsu ga masoyansu da suka ba su damar samun nasara a zaben da aka yi.

“Abin murna da samun ci gaba mai ma’ana, sakamakon ci gaba da kula da Kogin Rabbit Hash, sannan za mu ci gaba da yin maraba ga baki don ziyartar garin da ake zuwa nishadi a shekaru masu yawa”, inji Amy.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7