An zabi sababbin shugabannin PDP na Sakkwato

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato ta zabi sababbin shugabaninta da za su ja ragamar jam’iyyar na shekaru hudu masu zuwa. An zabi Bello Aliyu Goronyo a matsayin Shugaba inda ya maye gurbin babban na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru Bafarawa, Alhaji Ibrahim Milgoma. Gwamnatin Filato ta soke kwangilar aikin hanyoyi uku Yadda aka […]

An zabi sababbin shugabannin PDP na Sakkwato

Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tamuwal

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Sakkwato ta zabi sababbin shugabaninta da za su ja ragamar jam’iyyar na shekaru hudu masu zuwa.

An zabi Bello Aliyu Goronyo a matsayin Shugaba inda ya maye gurbin babban na hannun daman tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Attahiru Bafarawa, Alhaji Ibrahim Milgoma.

An zabi Alhaji Aliyu FC Mataimakin Shugaba, sai Sakatare Alhaji Zaki Bashire, da Alhaji Murtala Abdulkadir Dan’iya a matsayin Ma’aji wanda ya maye gurbin kanin Alhaji Attahiru Bafarawa, Alhaji Nasiru Bafarawa.

Hajiya Kulu, ’yar Sardauna ce jam’iyyar ta zaba Shugabar Mata, sai Mustafa Binji Shugaban Matasa da sauran mukamai 39.

A jawabin Gwamna Aminu Tambuwal bayan kammala taron ya gode wa tsohon Shugaban Jam’iyyar, Alhaji Ibrahim Milgoma wanda ya ce jagora ne nagari jajirtacce da ya yi aiki tukuru don ganin PDP ta samu  nasara.

“Ba shakka jarumi kake, kai mai amana ne ban da sha’anin tsarin mulkin jam’iyya ina tabbatar maka cewa da kai ne za ka wuce, amma mun san cewa a tsarin jam’iyya ba zai yiwu mutum ya wuce zango biyu ba.

“Muna tabbatar maka tafiyarmu ta amana ce za mu tafi tare da kai,” inji Gwamna Tambuwal.

Jami’in hulda da Jama’a na Jam’iyyar, Alhaji Yusuf Abdullahi Hausawa ya ce su a matakin jam’iyya ba su dauki wani na hana wa wani samun mukami ba.

“Matsayarmu Allah ne bai kaddara tsohon shugaba ya dawo ba, ba wani mutum da zai hana masa dawowa,” inji Hausawa.