An zabi sababbin shugabannin Wakilan jaridu reshen Jigawa

An zabi shugabannin kungiyar Wakilan Kafafen Watsa Labarai (Correspondent’s Chapel) ta kungiyar ’Yan jarida ta kasa reshen Jihar Jigawa.Zaben wanda aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata, ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban kungiyar Malam Abdullahi Yakubu na jaridar Thisday daga mukaminsa sakamakon zarginsa da rashin adalci da ’ya’yan kungiyar suka yi.Suna yin […]

An zabi sababbin shugabannin Wakilan jaridu reshen Jigawa
An zabi sababbin shugabannin Wakilan jaridu reshen Jigawa

An zabi shugabannin kungiyar Wakilan Kafafen Watsa Labarai (Correspondent’s Chapel) ta kungiyar ’Yan jarida ta kasa reshen Jihar Jigawa.
Zaben wanda aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata, ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban kungiyar Malam Abdullahi Yakubu na jaridar Thisday daga mukaminsa sakamakon zarginsa da rashin adalci da ’ya’yan kungiyar suka yi.
Suna yin murabus sai kungiyar ta kafa kwamatin gudanar da zabe a karkashin jagorancin Abdullahi Onako na jaridar Daily Trust sai Bayo Alabira ya zama sakataren kwamitni sai Munkaila Tsoho na jaridar The Sun wakili.
Malam Abdullahi Shugaba na Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a matsayin sabon shugaban kungiyar sai Aliyu Hamagam na jaridar Daily Trust, Mataimakin Shugaba sai Mustapha Isma’ila na Kamfanin NAN, Sakatare sai Umar Akilu Majeri na jaridar Aminiya, Ma’aji, yayin da Tina Anthony Akannam ta jaridar banguard ta zama Mai Binciken Kudi ta kungiyar, inda kowannensu ya samu kuri’a 13 daga cikin kuri’a 20 da aka kada.
Mai shari’a Baffa Alhassan ne ya rantsar da sababbin shugabannin bayan gudanar da zaben a gaban jami’an tsaro da manema labarai da wakilan da suka fito daga gidan talabijin na NTA da Rediyon Jigawa da rediyon Freedom da wakilan Ma’aikatar Wasta Labarai ta Tarayya.