An zabi sabbin shugabanni a Kasuwar Wunti da ke Bauchi

kungiyar ’Yan Kasuwar Wunti da ke Jihar Bauchi ta gudanar da zaben shugabanninta kwanakin baya wadanda za su jagoranci kungiyar na tsawon shekara hudu kafin daga bisani a sake zaben wasu shugabannin.Wadanda aka zaba sun hada da Alhaji Iliyasu Nuhu a matsayin shugaba da Alhaji Gambo Muhammed a matsayin mataimakinsa. Har ila yau, an zabi […]

An zabi sabbin shugabanni a Kasuwar Wunti da ke Bauchi
An zabi sabbin shugabanni a Kasuwar Wunti da ke Bauchi

kungiyar ’Yan Kasuwar Wunti da ke Jihar Bauchi ta gudanar da zaben shugabanninta kwanakin baya wadanda za su jagoranci kungiyar na tsawon shekara hudu kafin daga bisani a sake zaben wasu shugabannin.
Wadanda aka zaba sun hada da Alhaji Iliyasu Nuhu a matsayin shugaba da Alhaji Gambo Muhammed a matsayin mataimakinsa. Har ila yau, an zabi Alhaji Muhammadu Mai Samira a matsayin ma’aji da Auwal Shu’aibu Dauda a matsayin sakatare. Sai mataimakin sakatare Suleiman Suleiman da kuma Alhaji Abubakar Abdullahi a matsayin sakataren kudi.
Hakazalika, Khalik Muhammed shi ne mai binciken kudi, Mika’il Abdullahi sakataren jin dadi da Alhaji Aminu Saleh sakataren tsare-tsare sai kuma Alhaji Abdullahi Isa a matsayin jami’in yada labarai.
Da yake zantawa da Aminiya a wajen rantsuwar kama aiki sabon shugaban kungiyar ya bayyana cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen hada kan daukacin ‘yan kasuwar baki daya.
“Da wadanda suka yi nasara da wadanda ba su yi ba, dukkansu mambobin kungiya ne kuma zan yi adalci daidai bakin gwargwadona domin yanzu ni na kowa ne,” inji shi.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya