An zabi sabon shugaban kungiyar masu shayi ta jihar Filato

’Ya’yan Kungiyar Masu Shayi ta Kasa reshen Jihar Filato, sun zabi Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu a matsayin sabon Shugaban Kungiyar. ’Ya’yan kungiyar masu shayin sun zabi sabon shugaban nasu ne, a karshen makon jiya a garin Jos, babban birnin Jihar Filato. Da yake jawabi bayan kammala zaben shugaban kungiyar masu shayi ta Najeriya Alhaji […]

An zabi sabon shugaban kungiyar masu shayi ta jihar Filato

Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu

’Ya’yan Kungiyar Masu Shayi ta Kasa reshen Jihar Filato, sun zabi Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu a matsayin sabon Shugaban Kungiyar. ’Ya’yan kungiyar masu shayin sun zabi sabon shugaban nasu ne, a karshen makon jiya a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

Da yake jawabi bayan kammala zaben shugaban kungiyar masu shayi ta Najeriya Alhaji Shu’aibu Abubakar ya bayyana matukar farin cikinsa, kan yadda aka gudanar da zaben lafiya.

Ya ce wannan zabe da suka gudanar ya zo musu da  sauki sosai,  domin an samu sulhu  tsakanin ’yan takarar.

Ya yi kira ga sabon shugaban ya rike wannan amana da adalci musamman ganin yadda ’ya’yan kungiyar suka taru suka zabe shi a matsayin shugaba.

Ya kuma yi kira ga sabon shugaban ya tashi tsaye wajen ganin ya kwato wa ’ya’yan kungiyar hakkokinsu a wajen hukumomi da kamfanonin da suke sarrafa kayayyakin shayi.

Sai ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su bai wa sabon shugaban goyon baya da hadin kai domin ya samu nasarar ayyukan da ke gabansa.

Daga nan ya yi kira ga ’ya’yan kungiyar su rike wannan sana’a tasu da daraja domin sana’a ce mai matukar muhimmanci a duniya.

A jawabin sabon shugaban  Malam Abubakar Ibrahim Madaki Mangu ya bayyana cewa ya yi matukar farin ciki da wannan zabe da aka yi masa.

Ya ba da tabbacin cewa zai yi iyakar kokarinsa wajen ganin an bi dokoki da tsarin wannan kungiya a kan wannan matsayi da aka zabe shi. Ya ce asalin kafa wannan kungiya shi ne masu shayi su taimaki junansu, don haka ya ce za su yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun taimaki junansu.

Ya yi kira ga dukan ’ya’yan  kungiyar su ba su goyon baya da hadin kai don ganin sun samu nasarar kudirorin da suka sanya a gaba.

Wakilan kungiyar da suka gudanar da zaben, sun fito ne daga kananan hukumomin  Kanke da Panshing da Kanam da Bokkos da Mangu da Barikin Ladi da Bassa da Jos ta aAewa da kuma Jos ta Gabas, da ke Jihar  Filato.