An zabi Tijjabi Babangida a matsayin mataimaki na musamman ga Sunday Oliseh
Tsohon dan kwallon Super Eagles Tijjani Babangida ne aka zaba a matsayin mataimaki na musamman ga sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles watau Sunday Oliseh. An zabo Babangida ne tare da wadansu don taimaka wa kocin don ganin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta kai ga gaci.Babangida wanda zai zama jami’in tuntuba […]
Tsohon dan kwallon Super Eagles Tijjani Babangida ne aka zaba a matsayin mataimaki na musamman ga sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles watau Sunday Oliseh. An zabo Babangida ne tare da wadansu don taimaka wa kocin don ganin kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta kai ga gaci.
Babangida wanda zai zama jami’in tuntuba (liason officer) zai hada ayyuka biyu ne watau na taimakawa kocin wajen bayar da shawarwari da kuma na yin hulda da jama’a.
Tijjani Babangida ya taba yin kwallo a kulob din Ajad da ke Holland da Sunday Oliseh kuma suna daga cikin ’yan kwallon da suka yi wa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da ya gudana a shekarar 1998.
Tijjani Babangida ya taba zama Manajan kulobh din Taraba United kafin su raba gari.