An zarge shi da kashe matarsa da tsohon ciki

Ana zargin wani magidanci mai suna Habibu da ke garin Dingim, yankin karamar Hukumar Minjibir da laifin  kashe  matarsa mai suna Aina’u, ’yar  shekara 26, wadda kuma suke da ’ya’ya biyu maza da kuma tsohon  ciki.Wakilinmu wanda ya yi tattaki zuwa gidan iyayen matar da aka kashe da ke garin Kunya, Unguwar Kaukai-Makadi, cikin yankin […]

An zarge shi da kashe matarsa da tsohon ciki
An zarge shi da kashe matarsa da tsohon ciki

Ana zargin wani magidanci mai suna Habibu da ke garin Dingim, yankin karamar Hukumar Minjibir da laifin  kashe  matarsa mai suna Aina’u, ’yar  shekara 26, wadda kuma suke da ’ya’ya biyu maza da kuma tsohon  ciki.
Wakilinmu wanda ya yi tattaki zuwa gidan iyayen matar da aka kashe da ke garin Kunya, Unguwar Kaukai-Makadi, cikin yankin karamar Hukumar Minjibir, kuma  ya tattauna da mahaifin  marigayiyar, Alhaji Yahaya Kiri  da yayanta, Sa’idu Ilaye da kuma danta mai shekaru 6 mai suna Sadik, wanda aka yi kisan a gabansa domin jin yadda lamarin ya faru.
Da farko yayan marigayiyar, Sa’idu Ilaye ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da auren Aina’u ya mutu da Habibu sai ta kai kararsa kotu bisa maganar kudin ciyarwa, wanda daga nan ne ake zaton matsalar ta samo asali, duk da cewa daga baya ya sake mayar da ita gidansa, duk da cewa suna zaune ne ba tare da jituwa mai kyau ba.
Ya ce ganin irin zaman da suke yi na rashin jituwa kuma baya kwana a gidan da take, sai Aina’u ta sake shigar da kara tana kalubalantar matakin da ya dauka na rashin kwana a inda take sai gidan daya matar tasa tun da su biyu ne. Ya kara da cewa lokacin da aka kai wa mijin kanwar tasa takardar kira daga kotu ranar Alhamis ta makon jiya, sai kuma aka wayi gari  da rasuwar ta  ranar Asabar  kuma aka yi jana’izarta a wannan rana.
Ya kara da cewa, tun kafin a yi jana’izar kanwar tasa ya lura cewa akwai sawun duka a fuskarta, wanda ya sa har ya tambaya amma da yake al’amarin bai zamo na bincike ba, sai ya kyale maganar kafin daga bisani zarge-zarge suka yi ta fitowa har daga karshe dagacin Dingim ya mika shi gidan hakimin Minjibir, inda kuma kafin ’yan sanda su je sai ya tsere bisa bukatar a bar shi ya je fitsari.
Ya ce sun bi shi bisa kokarin kamo shi tare da wani dan sanda amma ba su iya kama shi ba saboda babur din acaba da ya hau zuwa wani gari Tsakuwa, inda suka sake bin sa can amma nan ma aka ce masu ya sauka daga babur din kuma an ga ya yanka cikin daji, wanda daga nan ne ya bace.  
Shi ma mahaifin marigayiyar, Alhaji Yahaya, ya bayyana cewa kwana guda kafin rasuwar Aina’u  sai da ta kira shi a waya suka yi magana kan yanayin zaman da take yi da mijin nata, wanda kuma daga bisani  aka sanar masa da rasuwarta.
Da yake yin bayani ga wakilinmu, dan marigayiyar mai shekara 6, Sadik, ya ce bayan sun dawo daga gidan wani suna sun kwanta da babar tasu da kanensa  Mudi mai shekara 4, dayake gidan su kadai ne, sai kawai ya ga babansu yana dukan uwar tasu da tabarya tare da zungurinta a ciki duk da cewa tana da juna biyu, tana kuka da salati har ta daina motsi.
Daga nan sai ya dauke ta ya kai ta wani karamin daki, ya shimfide, kana ya haura katanga ya gudu.
Wakilinmu ya gano cewa har lokacin aiko da wannan labari ba a kama wanda ake zargin ba, sai dai an tsare iyayensa domin bincike a kokarin da ake yi na kama shi.