An zarge ta da kashe Sarki a ranar da zai mata kishiya
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta tsare matar Mai martaba sarkin Mama da aka fi sani da Gom Mama, Alhaji Zubairu Adamu da ke yankin raya kasa na Farin Ruwa a karamar Hukumar Wamba, tare da ’yarta da kuma wadansu mutane uku, ciki har da daya daga cikin dogarawan sarkin, dangane da zargi da take […]

Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta tsare matar Mai martaba sarkin Mama da aka fi sani da Gom Mama, Alhaji Zubairu Adamu da ke yankin raya kasa na Farin Ruwa a karamar Hukumar Wamba, tare da ’yarta da kuma wadansu mutane uku, ciki har da daya daga cikin dogarawan sarkin, dangane da zargi da take musu cewa sun kashe Gom Mama ta hanyar zuba masa guba a abinci.
Wakilinmu ya ziyarci kauyen Mama, inda lamarin ya auku, don gano gaskiyar lamarin, inda ya nemi ya gana da iyalan mamacin, amma hakan ya ci tura, don suna cikin makoki, suna masu nuni da cewa a halin yanzu ba za su iya cewa komai game da lamarin ba.
Shi ma Sarkin Wamba, Alhaji Musa Nagogo da Aminiya ta tuntube shi ya ki magana a kan lamarin. Sai dai wani wanda lamarin ya auku a idanunsa kuma daya daga cikin hadiman gidan marigayin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilimu cewa, “Shi dai marigayi Gom Mama, Alhaji Zubairu Adamu ya rasu ne a ranar 15 ga wata Fabrairun da ya gabata, wanda ya zo daidai da ranar da za a daura aure da matarsa ta biyu. Ya rasu ne a fadarsa da ke Mama. Bayan mutuwarsa, sai aka fara shirye-shiryen binne shi. Ana cikin shirye-shiryen ne sai Sarkin Wamba, Alhaji Musa Nagogo ya ba da umarnin cewa kada a binne gawar mamacin, don a cewarsa, yana so a bincika a gano abin da ya sa bakin mamacin yake fitar da kumfa bayan ya mutu. Daga nan sai ya shawarci iyalan mamacin su kai shi babbar asibitin koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH) don a auna a gano abin da ya yi sanadin mutuwarsa don a san matakin da za a dauka kafin a binne shi.”
Ya ci gaba da cewa, “Kafin ma a kai wannan gawar asibiti a garin Jos, an gano wadansu kwalaben magungunan kashe kwari da allurai da dai wadansu kayayyaki da bai kamata a ce an gansu a dakin da mutum ke kwanciya ba, a dakin wace ake zargin. Haka ne ma ya sa da dawowar iyalan mamacin daga garin Jos, sai suka sanar da ’yan sanda, inda suka kama matar mamacin suka tsare ta, daga baya ’yan sandan suka sake dawowa gidan suka kama ’yarta da wadansu mutane uku, ciki har da daya daga cikin dogarawan sarkin, aka kai su hedkwatar rundunar ’yan sanda da ke Lafiya, inda daga bisani muka samu labari cewa an wuce da su Makurdi ta Jjihar Binuwai, inda ake cigaba ta gudanar da bincike a kan aukuwar lamarin”.
Da wakilimu ya tambaye shi ko kafin mutuwar Sarkin akwai wani sabani a tsakaninsa da matarsa, sai ya ce, “A gaskiya dai babu wata matsala tsakaninsu lokacin da yake raye, domin marigayi Gom Mama mutum ne mai son zaman lafiya, kuma mai hankali, ba shi ma da lokacin fada da wani balle iyalansa. Amma daga baya-bayan nan, tun da matar ta gano cewa yana shirin kara aure, sai suka fara samun sabani a tsakaninsu, wanda na tabbata hakan yana faruwa ne saboda shirin aure da yake yi a lokacin. Don, kamar yadda na bayyana maka, ba su saba fada ba a da, amma tun da ya fara shirye-shiryen aure suna ta yi fada kafin mutuwarsa.”
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Umaru Isma’il ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin da a halin yanzu suke tsare a hannun ’yan sanda a Lafiya, ciki har da dogarin sarkin da ake zargin cewa da shi aka hada baki aka kashe sarkin, a gaban kotu da zarar rundunar ta kammala bincike a kansu.
Ya ce idan aka same su da aikata wannan laifi, to babu shakka za a hukunta su daidai da yadda doka ta tanadar. Daga nan sai ya gargadi al’ummar jihar baki daya su guji daukar doka a hannunsu, domin kuwa rundunarsu a shirye take ta hukunta duk wanda aka samu da irin wannan laifin.