An zargi Dagacin Kwarsa da kokarin kwace gonakin talakawa

Wani manomin shinkafa a Gundumar Yalwan Damai a Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa mai suna Malam Adamu Sule Kankau ya koka kan zaluncin da ya ce sarakuna suke kokarin yi masa na kokarin raba shi da gonarsa. Malam Adamu Kankau ya zargi Dagacin Kwarsa da ke karkashin Hakimin Yalwan Damai Malam Umar Madaki […]

An zargi Dagacin Kwarsa da kokarin kwace gonakin talakawa

Gwamnan Badaru Abubakar na Jihar Jigawa

Wani manomin shinkafa a Gundumar Yalwan Damai a Karamar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa mai suna Malam Adamu Sule Kankau ya koka kan zaluncin da ya ce sarakuna suke kokarin yi masa na kokarin raba shi da gonarsa.

Malam Adamu Kankau ya zargi Dagacin Kwarsa da ke karkashin Hakimin Yalwan Damai Malam Umar Madaki Kwarsa da kwace masa gonarsa da ya dogara da ita wajen ciyar da iyalansa ya sayar wa wani mai kudi a cikin garin Birnin Kudu.

Malam Adamu Kankau ya kara da cewa dagacin na Kwarsa ya jima yana raba talakawa da gonakinsu yana bai wa masu kudi kuma yana hada baki da wadansu miyagun alkalai da ’yan sanda wajen amfani da karfin gwamnati ana kwace musu gonaki ana ba masu karfi.

Malam Adamu ya ce yana noma shinkafa kamar buhu 100 duk shekara a gonar, amma aka kwace shekara biyu ke nan, kuma ya kai shi kara kotu amma kotun ta kasa amsar gonar.

Saboda haka ya bukaci Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammadu Nuhu Sunusi ya binciki maganar wajen ganin an dawo masa da gonar.

Kankau ya ce gonar gadonta ya yi daga wajen mahaifinsa Sulaimanu shi kuma ya gada daga wajen kakansu Malam Yusuf , amma dagacin ya ce wai gonar baitil mali ce.

Da yake kare kansa kan batun, Dagacin Kwarsa Malam Umar Madaki Kwarsa ya ce wancan wuri da Adamu Kankau yake magana na gwamnati ne kuma ba gona ba ce saboda haka ne ya kwace, inda ya kara da cewa Karamar Hukumar Birnin Kudu ce ta umarci ya kwace ba wai yin kansa ba ne saboda a cewarsa ba ya biyan harajin gona.

Hakimin Yalwan Damai Malam Sani Musa Dan Makwayon Dutse ya ce ba ya da masaniya kan lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne a lokacin hakimin da ya gabace shi.

Da yake yawabi, Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Alhaji Wada Faka ya ce suna da masaniya  kan zargin kama- karyar da dagacin ke yi yana amfani da sunan karamar hukumar yana cin zarafin jama’a saboda haka ya ce za su dauki matakin ladabtarwa  kan dagacin.

Alhaji Wada Faka ya ce irin wadannan dagatan ne suke haifar da rikici a tsakanin manoma da makiyaya saboda haka za su zauna da masarautar, sannan su dauki mataki mai kwari.