An zargi duba-gari da cin zarafin mata mai abinci a Kalaba

Wasu duba gari da Ma’aikatar kula da tsaftar gari ta dauka aiki sun ci mutuncin wata mata mai sayar da abinci da sauran kayan kwalama a wasu shagunan zamani da ke daura da gidan mai na Oando da ke Kalaba, a cewarta, ba tare da ta aikata laifin komai ba.Matar mai suna Grace Aship Francis, […]

An zargi duba-gari da cin zarafin mata mai abinci a Kalaba
An zargi duba-gari da cin zarafin mata mai abinci a Kalaba

Wasu duba gari da Ma’aikatar kula da tsaftar gari ta dauka aiki sun ci mutuncin wata mata mai sayar da abinci da sauran kayan kwalama a wasu shagunan zamani da ke daura da gidan mai na Oando da ke Kalaba, a cewarta, ba tare da ta aikata laifin komai ba.
Matar mai suna Grace Aship Francis, ta ce ba haka kawai ta fara sana’a a wurin ba sai da ta nemi izini daga hukumar amma sai ga shi an wayi gari jami’an hukumar duba garin sun rika dora mata asara.
Ma’aikatan dai sun ce suna aiki ne bisa umarnin shugabansu, kuma sun ki taba kayan matar sakataren ma’aikatar, wacce ita ma take sayar da abinci kusa da ita.
Matar, wadda cikin hawaye ta shaida wa Aminiya cewa: “Na kasa kayana kamar yadda na saba kullum, ranar nan ina kan bakin sana’ata, ina tsakar ciniki sai kawai jami’an duba gari suka wurgo leda cike da kashi cikin abincina na sayarwa, ba tare da yi mini wani jawabi ko kalami na dalilan daukar matakin hakan ba.” Inji ta. Ta ce a ranar abinci na Naira dubu 60 ta dafa kuma mafi rinjayen kayan ta karbo su ne a kasuwa wurin abokan hulda kan cewa sai ta ci kasuwa ta kai balas ta karbo wani.
Ta nuna wa Aminiya takardar shaidar iznin yin sana’a a harabar wurin da hukumar kula da tsaftar muhalli a Kalaba ta ba ta, mai lamba kamar haka: CU/fhs/19/25/14, mai dauke da kwanan wata 22/10/2015.
Ya zuwa yanzu dai Grace Aship Francis ta ce kudin jama’a da suka hau kanta yanzu haka ta wannan dalili sun haura Naira dubu 160. Ta yi fata gwamnati za ta duba lamarinta game da wannan gallazawa da t ace an yi mata.
Aminiya ta tuntubi Jo-Mary Eke Ita, daya daga cikin jami’an hukumar kare muhallin game da lamarin amma ya ce ba zai ce uffan ba.