An zargi gwamnatin baya da gaza kare hakkin Fulani
Shugaban sabuwar kungiyar matasan al’ummar Fulani ta kasa ta Jonde Jam, Alhaji Sa’idu Abdullahi Maikano ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata ba su iya yin komai ba wajen magance matsalolin da suke damun al’ummar Fulani a Najeriya.Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da sabuwar kungiyar tasu […]
Shugaban sabuwar kungiyar matasan al’ummar Fulani ta kasa ta Jonde Jam, Alhaji Sa’idu Abdullahi Maikano ya bayyana cewa gwamnatocin da suka gabata ba su iya yin komai ba wajen magance matsalolin da suke damun al’ummar Fulani a Najeriya.
Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da sabuwar kungiyar tasu da aka gudanar a garin Jos.
Ya ce an yi shekara da shekaru a Najeriya ana kashe Fulani, ana sace shanunsu amma abin takaici, babu wani mataki da gwamnatocin da suka gabata suka dauka, don magance wannan matsala da take ci masu tuwo a kwarya.
Ya kuma zargi kungiyoyin al’ummar Fulani da ake das u, cewa ba su yin abin da ya kamata na kare hakkoki da martabar al’ummar Fulani a Najeriya.
“Da kungiyoyin Fulanin nan suna yin abin da ya kamata a Najeriya, ya ya za a yi kan mutum daya da aka sace a Najeriya wanda ba a tabbatar da ko su waye suka sace shi ba; a ce za a kori al’ummar Fulani ga baki daya daga yankin Yarabawa?”
Ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari kan ya duba irin kisa da sace-sacen shanun da ake yi wa al’ummar Fulani a kasar nan.