An zargi jami’an tsaro da sakaci wajen kona kasuwar Bwari

Wasu ’yan kasuwa da sauran wadanda gobara ta shafa a kasuwar Bwari da ke yankin birnin Tarayya Abuja, sun danganta sakacin jami’an tsaro da lamarin, inda aka zargi wasu matasa daga kabilar Gbagyi da banka wa kasuwar wuta a ranar Litinin da ta gabata; bayan kashe wani dan kabilar da wasu kungiyar ’yan asiri suka […]

An zargi jami’an tsaro da sakaci wajen kona kasuwar Bwari

Wasu ’yan kasuwa da sauran wadanda gobara ta shafa a kasuwar Bwari da ke yankin birnin Tarayya Abuja, sun danganta sakacin jami’an tsaro da lamarin, inda aka zargi wasu matasa daga kabilar Gbagyi da banka wa kasuwar wuta a ranar Litinin da ta gabata; bayan kashe wani dan kabilar da wasu kungiyar ’yan asiri suka yi.

Wakilinmu da ya ziyarci kasuwar a ranar Talata da ta gabata, ya ga yadda wasu daga cikin ’yan kasuwar ke tattara ’yan abubuwan da suka yi saura daga gobarar, wadda ta kai ga kona ilahirin kasuwar baya ga wasu shaguna da ke kan titi da ke da kusanci da wajen, inda su ma matasan suka kona su.

Malam Halidu Muhammad, dan kasuwa ne da ke sayar da hatsi a kasuwar. Ya yi korafin cewa, “bayan dan lokaci da bude shagunanmu a ranar sai kawai muka fara jin hatsaniya daga waje. Da muka fita sai muka kula da wasu matasa na kona tebura da kuma shaguna da ke kan layin kasuwar. Nan take muka sanar da babban ofishin ’yan sanda da ke nan kusa da mu ta waya da kuma zuwa ofishin, amma abin mamaki ba su tashi zuwa ba sai bayan wajen awa daya da fara hatsaniyar. Sai dai kafin nan matasan sun cinna wa kasuwarmu wuta ta hanyar jefo kwalabe da ke dauke da fetur da suka cinna wa wuta da kuma tayu.

“A lokacin ne suka tarwatsa gungun matasan kafin motar kashe gobara da matasan suka hana ta isowa ta samu damar karasowa. Sai dai a lokacin wutar ta riga ta yi wa kasuwar illa, inda zuwansu bai yi wani tasiri ba, har dai wutar ta kona daukacin kasuwar gaba daya,” inji dan kasuwar.

Ifanyi Joseph wani mai sayar da kayan masarufi da lamarin ya shafa ya ce: “A lokacin da na samu labarin wutar da misalin karfe 12 na rana, ina tare da iyalaina a wajen bikin Kirsimeti a garin Dutse-Alhaji, inda nake da zama, sai dai ko da na iso nan ban iya daukar komai ba, kasancewar wutar ta riga ta kona daukacin kasuwar.”

Ya yi bayanin cewa ’yan kasuwa da dama sun gwammace barin kudi a cikin shagunansu a lokacin da suka tafi hutun Kirsimeti, kasancewar babu bankuna a ranakun da suka gabaci na gobarar, duk da irin ruwan ciniki da suka yi a lokacin.

Ya zuwa ranar Talata da ta gabata, adadin wadanda suka rasa rayukansu ya karu zuwa hudu daga mutum na farko da hukumomi suka tabbatar a farko, inda bayanai suka ce mutum na hudun ya gamu da ajalinsa ne a ranar Talata a lokacin da ya je wani yankin garin da ake kira unguwar Gbagy don dauko wasu kayansa, inda aka auka masa da sara da ta kai shi ga mutuwa, a yayin da wani kuma bayanin ya ce ya tsira da rauni.

Tuni dai Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ya ayyana dokar ta-baci a garin daga karfe 6 na dare zuwa 6 na safe. Kakakin Ministan, Malam Abubakar Sani wanda ya tabbatar da hakan a yayin zantawa da Aminiya a ranar Talatar, ya kuma ce jami’an tsaro sun kama wasu daga cikin wadanda ake zargi a lamarin.