An zargi kwamitin raba tallafi da zagon kasa a Jigawa

Kwamashiniyar mata da jin dadin jama’a ta Jihar Jigawa, Hajiya Ladi dansure ta nuna damuwarta game da yadda wasu ’yan kwamatin da aka dora wa alhakin raba awaki da murhunan girki suke wa shirin tallafa wa mata zagon kasa. Ta yi korafin cewa ’yan kwamatin da gwamnatin jihar ta kafa ba su yin aikinsu da […]

An zargi kwamitin raba tallafi da zagon kasa a Jigawa
An zargi kwamitin raba tallafi da zagon kasa a Jigawa

Kwamashiniyar mata da jin dadin jama’a ta Jihar Jigawa, Hajiya Ladi dansure ta nuna damuwarta game da yadda wasu ’yan kwamatin da aka dora wa alhakin raba awaki da murhunan girki suke wa shirin tallafa wa mata zagon kasa.

Ta yi korafin cewa ’yan kwamatin da gwamnatin jihar ta kafa ba su yin aikinsu da adalci, suna zaluntar gwamnatin jihar, wajen canja sunayen ainahi da sunayen ’yan uwansu da na matansu, maimakon wadanda gwamnatin jihar ta ce a tallafa ma wa
Kwamishiniyar ta yi Allah wadai da halayen ’yan kwamatin, wadanda ta ce saboda haka ne ta kafa wani karamin kwamati da zai sanya wa wancan babban kwamatin ido, idan za su yi ha’inci, ya tona masu asiri. Ta ce gwamnati ta kashe Naira miliyan 30 wajen tallafa wa matan da suke sana’ar abinci da Naira dubu ashirin kowacce da murhunan girki da awaki uku-uku.
Binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewa ba a raba wa mata kudin da sauran kayayyakin ba a yankin masarautar Dutse. A kan haka kwamashiniyar ta ce akwai dalili, domin sun gano cewa akwai wata matsala da ta yi wa shirin dabaibayi a yankin. Ta ce dalili ke nan ya sa aka dakatar da shirin ba da tallafin a yankin masarautar.
Kamar yadda bincike ya nuna, a yankin masarautar Hadeja kuwa an sami tabbacin cesa, wadanda aka ba tallafin awakin, sayarwa suka rika yi. Wasu kuwa yankawa suke yi suna cinyewa, da nufin cewa wai za su biya kansu wahalar da suka yi wa jam’iyyar APC.