An zargi malaman makarantar firamare da sakaci da aiki a Jihar Kaduna
Shugaban karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Lazuru ya bayyana cewa ya zama wajibi mutane su tsaya su sanya idanu a kan malaman da suke koyarwa a makarantun firamaren da ke yankunansu.Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen rufe gasar kacici-kacici da jami’in hulda da jama’a na kungiyar Ma’aikatan […]
Shugaban karamar Hukumar Lere da ke Jihar Kaduna, Alhaji Ibrahim Lazuru ya bayyana cewa ya zama wajibi mutane su tsaya su sanya idanu a kan malaman da suke koyarwa a makarantun firamaren da ke yankunansu.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi wajen rufe gasar kacici-kacici da jami’in hulda da jama’a na kungiyar Ma’aikatan kananan Hukumomi ta kasa (NULGE) reshen Jihar Kaduna, Kwamared Ahmed Tiyaye ya shirya wa makarantun firamare na karamar Hukumar Lere a garin Saminaka.
Ya ce dole ne a sanya ido kan malaman da suke koyarwa a makarantun firamare a kasar nan, domin da kudadensu ne ake biyan malaman albashi.
Ya yi korafin cewa wasu malaman ba su zuwa aiki, wasu kuma ba su san abin da suke koyar da yara ba. “Don haka duk mutanen da suke da makarantar firamare a kauyensu, suna da hakkin kula da malaman da suke koyarwa a makarantar, domin su ga suna koyar da yaransu irin abubuwan da ya kamata su koyar ko kuma su kai karar su zuwa gaba, domin da kudadensu ake biyan malaman albashi.” Inji shi.
Daga nan ya yaba wa wanda ya shirya wannan gasa, inda ya ce gasar babbar kalubale ce ga dukkan masu kishin bunkasa ilmi a yankin da kasar nan gabaki daya.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban Hukumar kananan Hukumomi ta Jihar Kaduna, Mista Asandu Garba ya shawarci iyayen yara kan su tabbatar cewa malaman da suke koyar da yaransu sun san abin da suke koyar da su. Ya yaba da wannan gasar da aka shirya wa makarantun, sannan ya yi kira ga masu hali da su yi koyi da wannan kokari, domin a samu bunkasa ilmi a yankin da kasa gabaki daya.