An zargi shugaban Cibil Defence da yi wa mata biyar fyade a ofishinsa

Wasu mata a garin Jega da Aliero a Jihar Kebbi sun zargi shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (cibil defence) na garin Jega Sani Anaruwa Suru da muguna musu tare da yi musu fyade a ofishinsa.Matan sun gabatar da kukansu ga kungiyar ci gaban Jega a makon jiya kamar yadda wata takarda da aka raba […]

An zargi shugaban Cibil Defence da yi wa mata biyar fyade a ofishinsa
An zargi shugaban Cibil Defence da yi wa mata biyar fyade a ofishinsa

Wasu mata a garin Jega da Aliero a Jihar Kebbi sun zargi shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (cibil defence) na garin Jega Sani Anaruwa Suru da muguna musu tare da yi musu fyade a ofishinsa.
Matan sun gabatar da kukansu ga kungiyar ci gaban Jega a makon jiya kamar yadda wata takarda da aka raba wa manema labarai da kungiyar ta rubuta wa karamar hukumar da hukumar cibil defense domin binciko gaskiyar al’amarin ta nuna.
Aminiya ta ziyarci sakatariyar karamar Hukumar Jega domin jin ta bakin shugaban karamar hukuma, inda ta tarar ya yi tafiya, amma ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa lallai sun samu wannan takarda koke amma a tuntubi mataimakinsa ko sakatarensa don jin cikakken bayani.
Da wakilinmu ya tuntubi mataimakin shu-gaban karamar hukumar Hassan Moham-med Dunbegu ya ce kungiyar ci gaban Jega ta kai wannan matsala ga ciyaman, kuma ya kafa kwamitin bincike don gano gaskiya lamarin.
Ya ce kwamitin ya kira wanda ake zargin ya zauna da shi inda aka bukaci ya kare kansa a rubuce.
Hassan Dunbegu ya ce zarge-zargen sun hada da yadda wannan babban jami’in tsaro ke danne kashi 70 cikin 100 na bashin da ya amso daga masu taurin bashi, inda yake ba masu kudin sauran kashi 30.
 Wata daga cikin matan da ake zargi ya yi wa fyade wadda ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa wakilinmu cewa wata mace da ke bin ta bashi ce ta kai kararta a ofishin Sani Anaruwa Suru, ta ce tana gida kwance da misalin karfe 11:05 mijinta ba ya nan sai aka yi sallama inda wani dan cibil defence da ake kira Yawuri ya ce su je ofis oga ya aiko ni an yi kararki a kan wasu kudi. Ta ce bayan da suka je ofis sai ya ce ta wuce dakinsa, inda ya y mata barazanar cewa idan ba ta amince ya yi lalata da ita ba, zai sa a yi mata wulakanci kuma a kulle ta na wata uku.
Ta ce bayan ya tilasta ta, sai kuma ya tilasta ta lalata da yaronsa Yauri, sannan ya ce a je a rufe ta, da gari ya waye ya yi mata tarar Naira dubu 30 da kuma biyan bashin da ke kanta kafin ya kyale ta.
Ta ce ’yan uwanta sun je neman beli ya hana, inda ta sake kwana ya sake lalata da ita shi da yaronsa.
Da wakilinmu ya tuntubi shugaban na cibil defence din da ake zargi ya ce wannan zargi ba gaskiya ba ne, wasu ne ke son a hada kai da su domin ganin ya bar garin Jega.
Ya ce shekarunsa 24 yana aikin gwamnati, wasu ne ke son kulla masa sherri, ya kuma ce  ya amsa wadannan zarge-zarge a rubuce.
Wasu rahotanni sun ce wasu shugabannin karamar Hukumar Jega ne ke daure wa jami’in gindi inda a wasu lokuta yake biyan basusukan da ke kansa.
kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin kwamanda hukumar na Jihar Kebbi ya ci tura inda aka shaida masa cewa ya tafi Abuja kuma har zuwa hada wannan rahoto bai dawo ba.