An zargi Sufeto Janar da saya wa matar Shugaba Buhari Jif biyu

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai da ke kula da rundunar sojan ruwa, Sanata Isa Hamma Misau (APC Bauchi), ya zargi Sufeto-Janar na ’yan sanda Ibrahim Idris da sayen motocin alfarmak irar Prado Jeep biyu ga matar Shugaban kasa, A’isha Buhari. Misau ya yi zargin ne lokacin da ya bayyana gaban kwamitin binciken rikicinsa da shugaban ’yan […]

An zargi Sufeto Janar da saya wa matar Shugaba Buhari Jif biyu

Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai da ke kula da rundunar sojan ruwa, Sanata Isa Hamma Misau (APC Bauchi), ya zargi Sufeto-Janar na ’yan sanda Ibrahim Idris da sayen motocin alfarmak irar Prado Jeep biyu ga matar Shugaban kasa, A’isha Buhari.

Misau ya yi zargin ne lokacin da ya bayyana gaban kwamitin binciken rikicinsa da shugaban ’yan sandan. Ya ce uwargidan Buhari ta aiko da bukatarta ta hannun jami’in tsaronta (ADC), inda ta bukaci motocin kirar Sienna da Hiace, amma sai Sufeto-Janar ya saya mata jifa-jifai biyu.

“Uwargidan Shugaban kasa ta aiko da bukatarta ta hannun jami’in tsaronta, inda ta bukaci a saya mata motoci kirar Toyota Hiace da Sienna. A ranar da jami’in tsaron ya rubuto bukatar, sai nan take Sufeto-Janar ya yi rubutun bayar da izinin a saya mata jifa-jifai gudabiyu. Kuma ba ya cikin ka’idar kasafin kudin da aka ware, tun da babu inda suka ce a saya wa Uwargidan Shugaban kasa motoci kirar Jeep gudabiyu,” inji shi.

Sannan ya yi zargin cewa Sufeto-Janar ya yi murda-mudar jirkita lokacin ajiye aikin manyan jami’an ’yansanda, inda ya sauya kwanan watan daga 3 ga Janairu zuwa 15 ga Janairun 2019.

Shugaban kwamitin da mataimakin mai ladabtarwa a Majalisa, Francis Alimikhena sun ce Sufeto-Janar zai gurfana a gaban kwamitin binciken a mako mai zuwa.