An zubar da jarirai 25 cikin wata shida a Bauchi

Talauci da guje wa abin kunya sun sa wasu ’yan mata da zawarawa a garin Bauchi zubar da jariransu a bola ko cikin masai da wuraren da ba su dace ba. Kuma ana ganin yawan mutuwar aure da rashin rike auren tsakani da Allah ne ke jefa irin wadannan mata cikin garari, inda ake samun […]

An zubar da jarirai 25 cikin wata shida a Bauchi
An zubar da jarirai 25 cikin wata shida a Bauchi

Talauci da guje wa abin kunya sun sa wasu ’yan mata da zawarawa a garin Bauchi zubar da jariransu a bola ko cikin masai da wuraren da ba su dace ba.
Kuma ana ganin yawan mutuwar aure da rashin rike auren tsakani da Allah ne ke jefa irin wadannan mata cikin garari, inda ake samun karuwar yawon ta zubar da suke yi.
Duk da cewa Jihar Bauchi na aiki da shari’ar Musulunci, kuma dakarun Hisbah na kai farmaki gidajen mata a garin Bauchi, kamar yadda Shugaban Hukumar Shari’a ta Jihar Malam Mustapha Baba Ilelah ya shaida wa wakilinmu bayan kamo wasu ’yan mata a gidajen badala da otel otel cikin dare.
Malam Mustapha Illelah ya ce suna gurfanar da irin wadannan mutane maza da mata amma duk da haka lamarin sai karuwa yake yi, musamman ganin yadda a wasu lokuta idan sun kai farmaki irin wadannan wurare da ake badala sukan kama wadanda ba a zaton za a same su a irin wannan harka.
Ya ce a wasu lokutan sukan kama maza masu iyalai da matan aure da kananan yara, kuma suna gurfanar da su a gaban kotu a yi musu tara ko dauri.
Wata mace da aka taba kamawa ta jefar da ’yarta a bola da aka sakaye sunanta, ta bayyana wa wakilinmu cewa tsananin talauci ya sa ta shiga yawon banza har ta samu ciki saboda mahaifinta ya bar aiki shekara biyu ba kudin sallama yayin da akasararin ’yan uwanta maza ba su da aikin yi.
Ta ce tana cikin fantamawa don neman abin rufin asiri sai ciki ya bayyana, kuma da ta ga ba yadda za ta yi ne ta jefar da ’yar saboda a lokacin ba ta iya rike kanta balle dawainiyar ’yar.
A bana kurum an tsinci jarirai sama da 25 da aka zubar kuma yawanci ba sa rayuwa saboda galabaitar da suke yi kamar yadda shugabar hukumar lura ta marayu da marasa galihu ta jihar Bauchi (ObCA) Hajiya Bahijja Mahmud ta bayyana. Ta ce matsalar zubar da jarirai tana ba su takaici sosai.
Tace suna lura da yaran har su tashi cikin koshin lafiya ta kuma nuna takaici kan irin zubar da jarirai a garin Bauchi, inda ta ce irin wadannan yara ba su cika rayuwa ba, saboda kamuwa da cutar nimoniya da sauransu.
Hajiya Bahijja ta kirayi masu wannan mummunar al’ada ta zubar da jariran da suka haifa, su rika kai su gidan marayu maimakon zubar da su suna mutuwa. “Za mu amsa mu ci gaba da lura da su, ya fi bata sunan jiha da mutanenta da irin wadannan mata ke yi. Haka iyaye su kara himma wajen gyara tarbiyyar ’ya’yansu, shugabanni da masu unguwanni da malamai su taimaka wajen ganin an samu raguwar irin wannan aiki na zubar da jarirai da ya damu jihar,” inji ta.