Ana amfani da agwagi a kasar Sin wajen noman shinkafa

Manoman shinkafa a kasar Sin sun fito da tsarin amfani da agwagwa a kauyen Zhuangding da ke garin Taiping da ke karkashin birnin Mishan a Arewa maso gabashin kasar Sin da ke Lardin Heilongjiang.Wannan sabuwar dabarar amfani da agwagwa wajen noman shinkafa, ana saki agwagwar ne cikin gona, inda za ta rika cin kwari da […]

Ana amfani da agwagi a kasar Sin wajen noman shinkafa
Ana amfani da agwagi a kasar Sin wajen noman shinkafa

Manoman shinkafa a kasar Sin sun fito da tsarin amfani da agwagwa a kauyen Zhuangding da ke garin Taiping da ke karkashin birnin Mishan a Arewa maso gabashin kasar Sin da ke Lardin Heilongjiang.
Wannan sabuwar dabarar amfani da agwagwa wajen noman shinkafa, ana saki agwagwar ne cikin gona, inda za ta rika cin kwari da yi wa shuka ciro. Kuma tsarin noman yana bayar da kariya ga muhalli, ta hanyar kauce wa amfani da sinadaran da ke damfare da magungunan kashe kwari, inda za a rika samun taki daga kashin agwagwa ba tare da an yi amfani da takin zamani ba.
Tun a bara mazaunan wannan kauye na Zhuangding suka fara amfani da sabuwar dabarar noman shinkafa, ta hanyar amfani da agwagwa, kamar yadda jaridar Chinadaily ta ruwaito a cikin wannan makon.