Ana amfani da shafukan sada zumunta ana gurbata tunanin mutane – Obama
Tsohon Shugaban Amurka, Mista Barack Obama ya yi gargadi a kan yin amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ta hanyar da ta dace ba. Shugaban ya fadi a wata hira da ba kasafai yakan yi ba tunda ya sauka daga mulki a watan Janairu, cewa yin amfani da shafukan ba yadda ya dace […]

Tsohon Shugaban Amurka, Mista Barack Obama ya yi gargadi a kan yin amfani da shafukan sada zumunta na zamani ba ta hanyar da ta dace ba.
Shugaban ya fadi a wata hira da ba kasafai yakan yi ba tunda ya sauka daga mulki a watan Janairu, cewa
yin amfani da shafukan ba yadda ya dace ba yana gurbata tunanin mutane a kan al’amura masu sarkakiya da kuma yada labaran karairayi.
Mutumin da ya gaje shi, Shugaba Donald Trump, ya shahara wurin yin amfani da Twitter, ko da yake Obama bai ambaci sunansa a hirar ba.
Yariman Ingila, Harry ne ya yi hira da tsohon Shugaban Amurkar a madadin shirin Radio 4 na BBC, kamar yadda sashin Hausa na BBC ya ruwaito a shekaranjiya Laraba.
Yariman, wanda shi ne na biyar a cikin jerin masu jiran gadon sarautar Birtaniya, na cikin masu gudanar da shirye-shirye a shirin Radio 4 tsawon lokacin bukukuwan Kirsimeti.
Tsohon Shugaban Amurkar ya kuma bukaci masu rike da madafun iko su rika yin taka-tsantsan kan irin sakonnin da suke wallafawa a shafukan zumunta, yana mai cewa shafukan na kawo matsala game da rayuwar jama’a.
Obama ya bayyana takaicinsa kan yadda ake maye gurbin labarai na gaskiya da labaran kanzon-kurege, a shafukan da kuma yadda mutane ke karantawa ko sauraren abin da kawai zai gamsar da ra’ayinsu ba tare da tantance sahihancinsa ba.