Ana bai wa matar da ta haihu Naira miliyan daya da dubu 260 a Japan
Wani gari da ke karkarar kasar Japan, Nagicho, yawan al’umarsa ya ruvanya saboda tallafin haihuwa da ake bai wa duk matar da ta haihu da ya kai Fukuda ¥300,000 ($3,530), wato Naira miliyan daya da dubu 260 da zarar ta haihu, kamar yadda Misis Yuki Fukuda ta bayyyana wa Mujallar tattalin arziki ta ‘The Economist.’ […]

Wani gari da ke karkarar kasar Japan, Nagicho, yawan al’umarsa ya ruvanya saboda tallafin haihuwa da ake bai wa duk matar da ta haihu da ya kai Fukuda ¥300,000 ($3,530), wato Naira miliyan daya da dubu 260 da zarar ta haihu, kamar yadda Misis Yuki Fukuda ta bayyyana wa Mujallar tattalin arziki ta ‘The Economist.’ Al’amarin garin ya yi matukar daukar hankalin manema labarai, musamman saboda sanin cewa a kasar Japan tun daga shekarar 1955 al’ummar kasar ke raguwa, ta yadda yawan mace-mace ya fi haihuwar da ake yi. Kuma Firayiministan kasar Mista Shinzo Abe na shirin zuba dimbin kudin tallafawa wajen kula da lafiyar jarirai, saboda dimbin al’ummar kasar tsofaffi nee wadanda sshekarunsu suka zarta 65.
Wasu tsibin gidaje da ke kasan tsauni a Nagicho sun daidai tamkar yadda gari yake a kasar Japan. Da aka bi kadin al’amuran mutanen garin sai aka fahimci wani al’amari mai ban-mamaki kan hayayayafar jarirai. Yuki Fukuda na daya daga cikin iyaye mata da ke da ’ya’ya uku. Kumburin da ya bulluko daga jibgegiyar rigar sanyinta na nuni da cewa ta kusa haihuwar wani jaririn, al’amarin da aka ta’allaka shi da shirin tallafin dawainiyar jarirai da ta haifar ruvanyawar haihuwa tun daga shekarar 2005.
Ba abin mamaki ba ne ganin yadda masu daukar rahotannin ke kai-kawo a wannan karkara da ke wani sako a kasar don gane wa idanonsu kan ko akwai wani abu a ruwan da ke gangarowa daga tsaunin Nagi mai tasiri wajen hayayyafa. Dalilin dai a bayyane yake karar, wato tallafin tattalin arziki. Domin damuwa da karancin ’ya’ya ta sanya karamar hukuma ta kara tallafin jarirai. Don haka yawan haihuwa ya karu daga ma’auninsu na 1.4 (ma’ana a samu yara 1.4 a rayuwa)r mace na tartibitin abin da ake bi a matakin kasa) sai ya daga zuwa 2.8 a shekarar 2014.
Misis Fukuda za ta samu kyautar Misis Fukuda ¥300,000 ($3,530), wato Naira miliyan guda da dubu 260 da zarar ta haihu. Kuma akwai tallafin rainon jariri na ¥1,800, tare da rahusar tafiya da su a mota da sauran bukatunsu a kowace rana. Idan ’ya’yanta suka girma har sukai ga shiga makarantar sakandare za ta rika samun 90,000 a shekara kan kowane yaro, musamman ga mutnen da ke zaune a wuri mai nisa. Duk da cewa matalauta a kasar Japan kan biya kudin inshorar kula da lafiyarsu da kashi 30 cikin 100 (sai gwmanati ta biya musu sauran), amma a Nagicho ke biyan kasha 30 cikin 100 ga kannan yara.
Sauran tsare-tsaren tallafin na da matukar ban mamaki. Garin ya dogara ne ga dimbin masu aikin sa kai don gudanar makarantun kananan yara biyu. Harkokin kasuwancin da ake gudanarwa a garin ba a biyan kudin hayar rumfa ko wajen kasuwanci, tsarin kyautatawar da ta jawo manyan kamfanoni uku tun daga shekarar 2014, a cewar Yoshiataka Kumagai, wani jami’in hukuma da ake aiki a karamar hukuma. Sannan birnin kan bayar da sababbin gidajen kwana haya a farashi mai rahusa.
Mista Kumagai ya jajirce kan cewa daukacin wadannan al’amuran kyautatawa ne kawai suka bunkasa hayayyafa daga kashi 2 cikin 100 da aka sarayar na kasafin kudin garin da ya kai Y4bn zuwa kashi 3 cikin 100. Tamkar dubban al’ummpomin da ke ta raguwa a daukacin fadin Japan, wannan gari ya yi matukar zakuwa, acewarsa: Nagicho ya yi asarar kashi uku na yawan al’ummarsa cikin shekarar 1955, kuma kashi uku na mutu 6,100 na mazaunan garin har yanzu masu shekaru ne da suka haura 65. “Muna kokarin maye gurbin mutum dubu shida,” inji shi.
Abin damuwar wannan gari daidai yake da na daukacin fadin ksar. Yawan mace-mace ya zarta haihuwa, inda alkaluma suka nuna cewa kiyasin gwamnati na shekarar 2016 akwai mutum 300,000 daga cikin al’umma mutum miliyan 127 za su ragu da kashi uku nan da shekaru 50 masu zuwa. Shi ya sa Firayiminista Shinzo Abe ya yi alwashin bunkasa yawan hayayyafa zuwa 1.8. Don cimma manufar za a kashe tiriliyan biyu na kudin kasar (Y2trn) na tallafi da majalisar mulkin kasar ta amince a watan da ya wuce, kudin da za a yi amfani da su wajen harkokin ilimi da kula da lafiyar yara.
Ko za a iya kwata wannan tsari na Nagicho a wani wurin daban? Horoko Kaiharta, wand aya koma garin shekarun da suka gabata da ’ya’yanta uku, inda take aiki makarantar rainon yara.na ganin hakan ba za ta yiwu ba.. Akwai tsaikon tafiyar hawainiya a rayuwa da ke daukar hankali da ban sha’awa; balamari ne mai sauki ba a samar da irin wadannan managartan tsare-tsare.” Misi Fukuda ta ce tana ta kokarin gano dalilin da ya sa iyalai ke kara yawa. Kudin na taimakawa,, a cewarta, amma wannan ba shi kadai ne dalilin ba. Ta yiwu akwai wani sinadari a ruwan (garrin da ke kwarara daga tsaunin Nagicho).