Ana barazaanar kashe alkali a Ghana

Wani alkalin Babbar Kotun kasar Ghana, Mai Shari’a Paul Dery wadda sunansa yake cikin alkalan da binciken  Anas Armaya’u Anas ya bankado da karbar cin-hanci kwanakin baya, ya rubuta wasika ga shugaban kasa game da barazar kashe shi da aka yi a shafin Facebook wadda jaridar Daily Graphic ta ruwaito. Mai shari’ar wanda ya ce […]

Ana barazaanar kashe alkali a Ghana
Ana barazaanar kashe alkali a Ghana

Wani alkalin Babbar Kotun kasar Ghana, Mai Shari’a Paul Dery wadda sunansa yake cikin alkalan da binciken  Anas Armaya’u Anas ya bankado da karbar cin-hanci kwanakin baya, ya rubuta wasika ga shugaban kasa game da barazar kashe shi da aka yi a shafin Facebook wadda jaridar Daily Graphic ta ruwaito.
Mai shari’ar wanda ya ce yana cikin matukar damuwa ya ce, yana zargin wani mutum mai suna, Cephas, da yin barazana ga rayuwarsa.
“Saboda haka ne nake rokon  Shugaban kasa ya yi amfani da ofishinsa mai daraja, ka sa ayi bincike game da barazanar. Ina fata da kyautata zaton zaka dauki matakin gaggawa game da wannan kuka na wa, ganin ina fargaba game da rayuwata,” inji shi.
Mai Shari’a Dery dai yana cikin jerin alkalan Babbar Kotun nan da ake zargi da hannu a cin-hanci da hana yin hukuncin gaskiya da adalci a kotunan  kasar Ghana.