Ana barazana ga rayuwata kan Fallasa ba fastoci kudi don goyon bayan Jonathan – Fasto Musa-Dikwa
Fasto Kallamu Musa Dikwa wanda ya fito ya bayyana wa duniya cewa Gwamnatin Tarayya ta ba fastoci Naira biliyan bakwai domin su goyi bayan Jonathan, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana tun daga lokacin da labarin ya bayyana. Kuma ya ce ba ya goyon bayan Shugaba Jonathan ko Janar Buhari, domin a ra’ayinsa dukkansu […]

Fasto Kallamu Musa Dikwa wanda ya fito ya bayyana wa duniya cewa Gwamnatin Tarayya ta ba fastoci Naira biliyan bakwai domin su goyi bayan Jonathan, ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana tun daga lokacin da labarin ya bayyana. Kuma ya ce ba ya goyon bayan Shugaba Jonathan ko Janar Buhari, domin a ra’ayinsa dukkansu ba su dace da shugabancin kasar nan ba:
Aminiya: Mene ne dalilinka na ganawa dan manema labarai?
Dalilin wannan ganawa shi ne a ranar Juma’ar da ta wuce na yi bayani a kan kudin siyasa da aka ba fastocin kasar nan wanda shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) suka raba. Tun daga lokacin da na yi wannan magana mutane suke ta cece-kuce. Wasu na zargina da cewa wai ina yi wa Buhari aiki ne. Shi ya sa na zo nan domin in sanar da jama’a cewa ba Buhari nake yi wa aiki ba, ba kuma shugaba Jonathan nake yi wa aiki ba. Saboda gaskiyar zance shi ne jama’armu ne ke mutuwa, mutuwar da mutanenmu ke yi shi ne damuwata, sannan Najeriya tana kara lalacewa. Saboda haka ba za mu yarda shugabannin da ke kawo mana matsala su ci gaba da shugabantarmu ba, bai kuma kamata mu yarda ba.
Aminiya: Kai ba ka ji dadin an ba da kudi ba ne ko ya saba wa koyarwar addinin Kirista ne?
Ya saba wa koyarwar addini, malaman addinan nan maimakon su karbi wannan kudi da sai su dubi matsalolin da ake fama da su. Misali dubi matsalar Boko Haram din nan da ke faruwa, kamata ya yi su matsa wa Shugaba Jonathan ya kama masu daukar dawainiyar ’yan Boko Haram a hukunta su, kada su karbi ko kwabo daga gwamnati. Abin da kawai ya dace shi ne su tabbatar sun sa an kama duk masu hannu a Boko Haram a yi masu hukuncin da dokar kasa ta tanada. Amma da yake a Najeriya babu doka saboda dokar a kan talakawa kadai ta tsaya ba su yi haka ba. Kuma ’ya’yanmu ne ake amfani da su ana ba su bindigogi kuma masu kudin ne da ’yan siyasa ke yin haka.
Aminiya: kungiyar CAN ta karyata zancen cewa an ba su wannan kudi, me za ka ce?
Mutumin da aka ba kudi ta hanyar da ba ta dace ba, idan sirrinsa ya bayyana kana ganin zai amince ya ce an ba shi ne? Amma dai Allah da ke sama Ya san an karbi wannan kudi.
Aminiya: Ka ce an raba miliyan uku-uku ga jihohi?
Kudin daga gwamnati suka fito, kuma akwai jihohi kusan hudu da suka tabbatar mana cewa sun karbi wannan kudi.
Aminiya: Wadanne jihohi ke nan?
Akwai Jihar Neja da Jigawa da Sakkwato, na rubuta dayan wanda na manta a yanzu.
Aminiya: Ko ana barazana ga rayuwarka saboda wannan bayani da ka fitar?
Barazana ba kadan ba, wasu suna fada min cewa zan mutu bada dadewa ba. Wasu kuma na fada min cewa ba su jin dadin abin da na fada ba. Amma ni dai abin da na sani da kuma yadda Ubangiji ke son in yi shi ne in yi gaskiya kuma in fadi gaskiya. Mu kuma kubutar da rayuwar mutane daga hannun masu kisa. Allah ba Ya son zubar da jinin talakawa, domin zubar da jinin talakawa zai kawo la’ana ga kasarmu.
Aminiya: Ko akwai kiran da za ka yi don ganin an kare ka daga wannan barazana?
Ubangiji na sama Shi ne ke kare ni, saboda haka ban nemi kariyar kowa ba. Na san mutane da yawa sun ji haushi, kuma da yawa suna cewa in yi hankali, na kuma fada musu cewa Ubangiji ne ke yi ba ni ba.
Aminiya: Fasto a ’yan takarar nan ka ce babu wanda ya dace ya shugabanci kasar nan, ko za ka kara wa jama’a bayani?
Dalili shi ne dukkansu halayyarsu da tafiyarsu sun nuna cewa ba su dace da mu ba. Idan muna son Najeriya ta gyaru dole mu samu shugabannin da ba su da tsassauran ra’ayi kuma ba su cin hanci da rashawa. Ba mu bukatar mutanen da za su kwashe dukiyar kasar nan su mayar da ita tasu ko masu fadin kalamai da ka iya jawowa ko haddasa rikici a tsakanin mabiya addinai a kasar nan.
Aminiya: Sakataren CAN na kasa ya ce ba su ma san ka a cikin kungiyarsu ba, me za ka ce?
Zai iya fadin haka, idan har shi Asake zai ce wai ban san ni ba, idan har yana jin tsoron Allah ya kamata ya nemi tuban Allah. Domin akwai lokacin da ya nemi cewa akwai abin da ake so in yi na kuma rubuta na ba su a rubuce saboda haka zancen ya ce bai san ni ba, bai taso ba.