Ana barazana ga rayuwata -Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung daya daga jiga-jigan kungiyar dattawan Arewa ne da ya bayyana aniyarsa ta neman zama dan takarar kujerar gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC , ya ce ana barazana ga rayuwarsa, inda har aka kai masa hari amma ya tsallake. Aminiya ta tuntube shi domin ya yi karin haske game da barazanar […]

Ana barazana ga rayuwata -Solomon Dalung

Barista Solomon Dalung daya daga jiga-jigan kungiyar dattawan Arewa ne da ya bayyana aniyarsa ta neman zama dan takarar kujerar gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC , ya ce ana barazana ga rayuwarsa, inda har aka kai masa hari amma ya tsallake. Aminiya ta tuntube shi domin ya yi karin haske game da barazanar da ya ce ana yi wa rayuwarsa, inda ya yi bayani kamar haka:

Aminiya: Mene ne cikakken bayani dangane da barazanar da ake yi wa rayuwarka?
Solomon Dalung: Abin da yake faruwa shi ne a wannan gwagwarmaya da nake yi ta fadakar da jama’a a kan zaman lafiya a kasar nan an sha yunkurin a halaka ni, ya kai kamar sau goma. Haka kuma bayan da na shigo wannan takara an kawo mini hari da makami aka bude mini wuta a kan hanyar Zariya, amma na gode Allah, domin babu abin da ya same ni a wannan hari da aka kawo mini. Kuma wannan abu da ya faru ba ’yan fashi ba ne, domin ni kadai suka auka wa, wadanda suke bi na a baya ba a yi musu komai ba. Wannan ya nuna cewa ni aka kawo wa hari.
Aminiya: A wanne lokaci ne aka kawo maka wannan hari?
Solomon Dalung: An kawo mini wannan hari ne kwanaki biyu kafin a kai wa Janar Muhammad Buhari hari a Kaduna.
Aminiya: A lokacin da aka kawo maka wannan hari ko ka sanar wa jami’an tsaro?
Solomon Dalung: Na sanar da jami’an tsaro a lokacin da aka kawo mini wannan hari, domin akwai ‘yan sanda da suke binciken motoci masu wucewa a hanyar. Na sanar da su abin da ya faru, suka bi ni muka je wurin da abin ya faru, suka duba ba su ga kowa ba. Daga nan suka dawo da shingensu wajen suka ci gaba da abin da suke yi na binciken motoci masu wucewa, ni kuma na wuce na ci gaba da tafiyar da nake yi.
Aminiya: Kana ganin ko wannan hari da aka kawo maka yana da danganta da wannan takara da ka fito?
Solomon Dalung: Babu mamaki a ce wannan hari da aka kawo mini yana da dangantaka da wannan takara ta gwamnan Jihar Filato da na fito. Ganin bayan kwanaki biyu aka kai wa Janar Muhammad Buhari hari a garin Kaduna. Kuma ina da masaniya cewa sunana yana cikin jerin sunayen mutum 1,000 da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce a cikin wasikarsa za a hallaka a lokacin zabe. Don haka wannan hari ba komai ba ne sai don wannan takarar da na fito.
Aminiya: Ko wannan hari da aka kawo maka zai karya maka gwiwa kan wannan takara da ka fito?
Solomon Dalung: Hausawa suna cewa idan aka bugi kura a kai an kara mata karfi ke nan, saboda haka wannan hari da aka kawo mini ya kara mini kirfin gwiwa ne a kan wannan takara da na fito.
Aminiya: Shugabannin jam’iyyarku ta APC reshen Jihar Filato suna cewa duk da ka fito wannan takara karkashin jam’iyyar sam ba ka kula da harkokin jam’iyyar ba, mene ne gaskiyar wannan magana?
Solomon Dalung: Ba na kula da harkokin jam’iyyar kamar ta yaya? Ni dan jam’iyyar APC ne. Wanne aiki ne suka ba ni wanda ban yi ba? Mene ne jam’iyyar ta ce na je na yi ban yi ba? Shugabannin jam’iyya fa ba sarakunan gargajiya ba ne. Su masu neman jama’a ne, masu neman wadanda za su kawo wa jam’iyya ci gaba ne. Saboda haka ban yi tsammanin akwai wani daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Filato da zai fito ya yi wannan magana ba.
Aminiya: Wadansu na zargin kana da alaka da Shugaba Goodluck Jonathan ka fito ne don ka yaudari mutane ne, a karshe za ka koma PDP. Yaya gaskiyar lamarin?
Solomon Dalung: Ni dai Allah Ya san ba ni da wata alaka da Shugaba Goodluck Jonathan. Kodayake sau da yawa yakan gayyace ni ya ce mini idan zan koma PDP zai ba ni duk wani matsayi da nake so, amma nakan gaya masa cewa ni dai ba zan amince da haka ba, don ba matsayi ko tara dukiya ne damuwata a rayuwa ba. Damuwata a kullum ita ce in kare hakkin dan Najeriya, musamman talaka. Shi ya sa ake kira na talaka. Saboda haka wannan magana ce kawai ta ’yan adawa, babu gaskiya ko kadan a wannan zargi cewa ina da alaka da Shugaba Jonathan.
Aminiya: To yaya gaskiyar batun da wadansu ke cewa jam’iyyarku ta APC jam’iyyar Musulmi ce kawai?
Solomon Dalung: To ina so masu wannan magana su tambayi kansu cewa su wane ne ke shugabancin jam’iyyar APC a kasar nan yau? Yau Kirista ne shugaban Jam’iyyar APC na kasa. Kuma akwai kiristoci da dama da suke rike da wadansu muhimman mukamai da dama a jam’iyyar. Saboda haka wannan magana ce kawai irin ta mahassada, wato ’yan PDP da suka kasa wajen gudanar da mulki nagari ga al’ummar kasar nan. Yanzu ga abin da ke faruwa a Arewa maso gabas. Ina daya daga cikin wadanda shi Jonathan ya nada don su shiga tsakani su sasanta tsakanin gwamnatin tarayya da su ’yan Boko Haram. Ka ga mun gaya masa cewa ga abin da wadannan mutane suke bukata don su ajiye makamansu. Amma ya ki amfani da wannan hanya. Ka ga shi Jonathan mutum ne da idan kana ba shi shawara zai kasa kunne sosai kamar wanda zai yi amfani da shawarar, amma a karshe sai ya yi watsi da ita. Shi ya sa ka ga wannan rigingimun Boko Haram da wadansu rigingimu da kasar nan ke fuskanta yau suka ki ci suka ci cinyewa, duk da cewa yana da damar magance su kacokan a duk lokacin da ya so. Saboda haka ba gaskiya ba ne cewa Jam’iyyar APC jam’iyyar Musulmi ne kawai, jam’iyyar kowa da kowa ce.
Aminiya: A karshe wacce shawara za ka ba al’ummar jihar nan?
Solomon Dalung: Don Allah a zauna lafiya da juna. Kada talaka ya bari wadansu ’yan siyasa su rika amfani da shi wajen tada zaune tsaye. Don su wadannan mutane da suke ba ka makami ka je ka kashe wani sun tura ’ya’yansu kasashen waje suna karatu. Amma kai ana nan ana amfani da kai kana kashe dan uwanka, jahilci kuma bai bar ka ka gane haka ba. A yi hakuri da juna a kuma fito a kada wa Jam’iyyar APC kuri’u a zabubbuka masu zuwa don kwato ’yancin talaka daga wurin shugabannin PDP da suka gaza wajen gudanar da shugabanci nagari a kasar nan baki daya. Na gode.