Ana bautar da kananan yara a Najeriya

Yadda ake amfani da yara masu kananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka hada da shagunan sai da kayan kawa ko abinci, otel otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko dakunan kwanan dalibai a jami’o’i (Hostel/Campus). Akasarin yaran ‘yan kasa da shekaru 15 ne kuma […]

Ana bautar da kananan yara a Najeriya
Ana bautar da kananan yara a Najeriya

Yadda ake amfani da yara masu kananan shekaru maza da mata don yin aiki ko bauta a gidaje da sauran wurare da suka hada da shagunan sai da kayan kawa ko abinci, otel otel, wuraren kwana na manyan makarantu ko dakunan kwanan dalibai a jami’o’i (Hostel/Campus). Akasarin yaran ‘yan kasa da shekaru 15 ne kuma ana daukarsu ne da nufin yin aikace-aikacen da suka hada da shara da wanke-wanke da wanki da goge-goge da debo ruwa da rainon jarirai da kula da yayayyun yara da makamantansu.
Mafi  yawan yaran ana kawo su cikin birni daga kauyuka lokaci zuwa lokaci, ta hanyar uwar aikatau bisa amincewar da yawa daga cikin iyayensu don tunanin samar musu da abin duniya da bai taka kara ya karya ba, musamman idan aka yi la’akari da irin illar da aikatau ke haifarwa a cikin al’umma.
Idan akai duba izuwa aikatau za a tabbatar da illolinsa masu yawa wadanda suke shafar yaran da ke yinsa da kuma yaran da iyayensu ke daukar ‘yan aikin kai har ma da sauran al’umma baki daya. Babbar matsalar ita ce  yadda ake tauye wa ‘yan aiki hakkinsu da ya  kamata su samu a lokacin kuruciyarsu. Misali, ilimi na daga cikin hakkin da ya  zama tilas a bai wa yara don inganta rayuwarsu da nufin samar da jagorori na gari a nan gaba, sai dai wannan dammar takan kubucewa akasarin ‘yan aiki, musamman yadda ake amfani da su wajen bautar da su a lokutan da ya  kamata a ce suna halartar makarantu don inganta rayuwarsu.
Na tabbata irin yadda ake maida su tamkar bayi a wasu wuraren ko kare ba a  yi masa haka, za ka ga ana yi musu tsawa ana hantararsu kai wasu har dukansu ake yi, a kuma hana su abinci, musamman in sun saba umarnin da uwar dakinsu ta ba su. Hakazalika in ka ga makwancinsu a wasu gidajen ko kajin gidan gona sun fisu wajen kwanciya mai kyau, ga rashin hutu da kuma rashin samun wadataccen barci wanda hakan ka iya yin barazana ga lafiyar jikinsu, kuma duk wannan kuncin ana biyansu wani dan abu da bai taka kara ya karya ba.
Wata babbar matsalar aikatau ita ce yadda jahilci ke addabarsu a inda yawayawansu ba su san yadda za su bauta wa Ubangijinsu ba, sai ka ga tsarki da cikakkiyar alwala na gagararsu kuma iyayen dakinsu basu cika damuwa da su  rika koyar dasu abubuwa masu amfani, musamman yadda za su rika gabatar da ibada tunda ta zama tilas a rayuwarsu, wannan yakan jawo musu ballagazanci da rashin kamun kai idan girma ya zo musu wanda ka iya jansu ga harkar banza, ko kuma yawon ta zubar don da yawansu ba su iya komawa karkararsu inda suka fito, mazan kuma su zamto marasa aikin yi wanda illarsa take da yawa a cikin al’umma. Kodayake ba duka aka taru aka zama daya ba, don kadan daga cikin iyayen dakinsu sukan turasu makarantun Islamiyya na Yamma ko na dare, amma akasari wannan bai cika samuwa ba. Haka kuma tsangwama da barazanar hukuncin muzantawa ko kuma kora gaba daya na zama fargaba a zukatansu.   
Kamar yadda na fada a baya illar aikatau takan shafi masu dauko su (Iyayen daki), don wasunsu sukan fita aiki ko makaranta tun safe sai yamma ko dare su bar ‘yar aiki da kula da yara kanana, wanda ita kanta ba ta da cikakkiyar tarbiyar da za ta kula da kanta ballantana har ta  koya wa yaran, a irin haka ne yaran kan tashi da dukkan abin da suka ga tana yi ko da kuwa marasa kyau ne.
Wata matsalar kuma ita ce yadda wasu masu gida ko yara matasa da ke gidan  kan lalata ‘yan aiki bisa tursasasu su amince da bukatarsu.
To meye abin yi don magance wandannan matsalolin? Su wa ke da alhakin kawo gyara akan wannan harkar?
A hakikanin gaskiya wannan matsalar tana bukatar hada hannuwa domin magance ta musamman yadda take barazanar lalata tarbiyar yara a matsayinsu na manyan gobe.
Da farko iyayen yaran na da mihimmiyar rawa wajen rage wannan matsalar, Kodayake halin kunci na talauci da daga cikin babban dalilin da ke jawo matsalar, amma duk da haka bai dace su rika bada ‘ya’yansu don kaiwa birni bisa rashin sanin takamaiman gidan da za a kai su da kuma halin da suke ciki a can ba. Kuma duk akan dan abin da bai kai ya kawo ba. Duk da a rayuwar duniya Allah da ya halicci bayinSa ya sanya wasu sun fi wasu, kuma wasu sai sun yi wa wasu aiki za su samu abin da za su ci, to in har ya zama dole ayi aikatau to iyayen yaran su sanya sharadi akan duk mai bukatar ‘yarsu don yin aikatau, to dole su sanya ta a makaranta don samun ilimi musamman don sanin yadda za su gabatar da addininsu.
Gwamnatoci da Hukumomin da ke da alhakin kare mutuncin yara su yunkuro don sanya kwakkwarar doka akan yadda ake azabtar da yara da sunan aikatau, a kuma sa doka mai tsauri ga duk wanda aka same shi da cin zarafi ko kuma bautar da yara. Haka kuma ya kamata gwamnatoci su rika kafa wuraren koyar da sana’o’i don yara maza da mata, musamman a yankunan karkara da suka hada da dinki da saka da rini da kere- kere da girke-girke da aikin kafinta da dai sauransu da nufin samar musu da madogara a gaba. Wannan zai hana su yawan fitowa neman abin duniya ta hanyar da ba ta dace ba.
A karshe jama’a su bada gudummawa don hana gurbata tarbiyar yara. Masu musguna wa ‘yan aikinsu su ma su ji tsoron Allah, su sani rayuwa ba ta da tabbas, don kuwa su ma yaransu ka iya kasancewa a irin wannan halin; kuma su lura da cewar duk abin da ka shuka shi za ka girba, don masu iya magana na cewa “yi alheri kaga alheri, in ka shuka irin sharri kuwa sharrin dai za ka girba a gaba”.
MUDASSIR ya rubuto daga NTA Zariya.
[email protected]

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno