Ana bautar ‘yar saniyar da aka haifa da ido daya ba hanci
Wasu mazauna wani kauyen Ranaghat a Jihar Bengal ta Yamma da ke kasar Indiya sun fara bautar wata ‘yar saniyar da aka haifa da ido daya ba hanci amma likitocin dabbobi sun ce, wannan ‘yar saniyar da aka haifa mai irin wannan halittar ba zat a yi tsawan rai na wasu makonni ba. Wannan ‘yar […]
Wasu mazauna wani kauyen Ranaghat a Jihar Bengal ta Yamma da ke kasar Indiya sun fara bautar wata ‘yar saniyar da aka haifa da ido daya ba hanci amma likitocin dabbobi sun ce, wannan ‘yar saniyar da aka haifa mai irin wannan halittar ba zat a yi tsawan rai na wasu makonni ba.
Wannan ‘yar saniyar mai ido daya, mazauna kauyen sun dauke ta tamkar wata abar bauta, don haka suke ta yunkurin zuwa wajen ta domin bauta mata.
Ita dai wannan ‘yar saniyar an haife ne da kwayar ido daya kawai a tsakiyan kanta babu hanci.
A yayin da uwar saniyar ke lasar ‘yar tata mai ido daya, su kuwa jama’ar garin sun hallara gabanta ne suna bauta mata a garin Ranaghat da ke Jihar Bengal ta Yamma, a Indiya.
Wani mazaunin kauyen Bengali da yake gaban ‘yar saniyar ya ce, “ Wannan ‘yar saniyar sauran gangar jikinta irin na sauran shanu ne, amma daga wuyanta zuwa kanta shi ne ya zama abin al’ajabi.”
Wata mata mazauniyar kauyen ta ce, “ban taba ji ko ganin irin wannan halittar dabbar ba a rayuwata.”
Mamallakin wannan saniyar da ta haihu kuma bai son a sanar da sunansa, ya ce “Makwabtan kauyenmu na ta zuwa gidana su na neman izinina, cewa za su bauta wa wannan ‘yar saniyar.”
Mutumin ya kara da cewa, “Duk tunaninmu shi ne wannan ‘yar saniyar wata mu’ujiza ce daga mahalicci. A bangaren mabiya addinin Hindu sun kwatanta ‘yar saniyar a matsayin wata sabuwar halitta da aka haifa a kauyen ta hanyar saniyar.”
Duk da yake ‘yan kauyen na bayyana irin abin mamakin da suka gani na haifar wannan ‘yar saniyar, likitocin dabbobi sun bayyana cewa, ana iya samun irin wannan halittar daga cikin hilittun masu rai da suke haihuwa wanda ake kira ‘cyclopia’ wato halitta mai ido daya. Kuma saniyar da ake haifa mai wata halitta ta ban al’ajabi na rayuwa ne kawai na wasu `yan makonni.