Ana bi-ta-da kulli ga ma’aikatan kananan hukumomin Yobe

Kimanin ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Yobe 500 aka dakatar da biyansu albashi a tsawon wata biyu da suka gabata, bisa zarginsu da kin zaben Gwamna Ibrahim Gaidam a zaben da ya gabata. Ma’aikatan a yanzu haka ana zargin an dakatar da ba su albashi na kusan wata biyu, kamar yadda wani rahoto da Aminiya ta […]

Ana bi-ta-da kulli ga ma’aikatan kananan hukumomin Yobe
Ana bi-ta-da kulli ga ma’aikatan kananan hukumomin Yobe

Kimanin ma’aikatan kananan hukumomin Jihar Yobe 500 aka dakatar da biyansu albashi a tsawon wata biyu da suka gabata, bisa zarginsu da kin zaben Gwamna Ibrahim Gaidam a zaben da ya gabata.

Ma’aikatan a yanzu haka ana zargin an dakatar da ba su albashi na kusan wata biyu, kamar yadda wani rahoto da Aminiya ta samu ya nuna. Rahoton ya nuna cewa hakan ya faru ne sakamakon zargin da gwamnatin jihar ke yi wa ma’aikatan da lamarin ya shafa na shiga harkokin siyasar da ta shafi jam’iyyar adawa ne ta PDP musamman a kananan hukumomin Karasuwa da Nguru da kuma Machina.
Wani ma’aikacin karamar Hukumar Nguru da wannan matsala ta shafa kuma ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa rabonsa da samun albashi tun watan Maris, ya ce da suka je karbar albashinsu an shaida musu cewa umarni aka bayar daga Damaturu a kan kada a biya su saboda ana zarginsa da kada kuri’unsu ga dan takarar Gwamna na Jam’iyyar PDP Alhaji Adamu Maina Waziri a zaben Gwamna, maimakon Gwamna Ibrahim Gaidam na Jam’iyyar APC.
Ya ce hakan bai dace ba, domin kowa mutum yana da ’yancin zaben wanda yake so, a matsayinsa na dan kasa ba tare da an tursasa shi ba.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Alhaji Dauda Yahya ya ce ba su san da wannan zargi ba, amma duk da haka zai bi diddigin wannan batu don gano abin da ya faru.
To, amma wani babban jami’in gwamnatin jihar da ya nemi a boye sunansa ya tabbatar da faruwar hakan, ya kuma ce a yanzu haka ana kokarin magance wannan lamari.