Kowane dan Najeriya zai biya bashin Naira 657,000

Ofishin Kula da Bashi na Ƙasa (DMO) ya bayyana cewa jimillar bashin Najeriya ya ƙaru da Naira tiriliyan 14.61 cikin shekara ɗaya, inda ya kai Naira tiriliyan 159.28

Kowane dan Najeriya zai biya bashin Naira 657,000

Kudi

Ofishin Kula da Bashi na Ƙasa (DMO) ya bayyana cewa jimillar bashin Najeriya ya ƙaru da Naira tiriliyan 14.61 cikin shekara ɗaya, inda ya kai Naira tiriliyan 159.28 a ranar 31 ga Disamba, 2025.

Wannan na nufin idan aka raba jimillar bashin Najeriya na Naira tiriliyan 159.28 da yawan al’ummar ƙasar (mutane 242,431,832), kowane dan Najeriya zai zai biya kimanin Naira 657,000.

Alkaluma sun nuna cewa bashin ya tashi daga Naira tiriliyan 144.67 da ake bin kasar a watan Disamba, 2024, wanda ya nuna ƙaruwa da kashi 10.1 cikin ɗari.

A ma’aunin dala, bashin Najeriya ya ƙaru daga dala biliyan 94.23 a Disamba, 2024 zuwa dala biliyan 110.97 a Disamba, 2025 — ƙaruwa da dala biliyan 16.75.

Jimillar bashin ya ƙaru daga Naira tiriliyan 153.29 a watan Satumba, 2025 zuwa Naira tiriliyan 159.28 a Disamba. Wannan ya nuna ƙaruwa da Naira tiriliyan 5.98 ko kashi 3.9 cikin ɗari.

Bashin cikin gida

Bashin cikin gida ne ya dauki kaso mafi rinjaye, inda ya kai kashi 53.27 cikin ɗari na jimillar bashin ƙasa a Disamba, 2025.

Yawan bashin ya tashi daga Naira tiriliyan 74.38 a Disamba, 2024 zuwa Naira tiriliyan 84.85 a Disamba, 2025 — ƙaruwa da Naira tiriliyan 10.47 ko kashi 14.1 cikin ɗari.

A cikin kwata kuma, ya ƙaru da Naira tiriliyan 3.03 daga Naira tiriliyan 81.82 da aka rubuta a Satumba, 2025.

A ma’aunin dala, bashin cikin gida ya ƙaru daga dala biliyan 48.44 a Disamba, 2024 zuwa Dala biliyan 59.12 a Disamba, 2025.

Gwamnatin Tarayya ce ta fi ɗaukar nauyin bashin cikin gida da Naira tiriliyan 80.49, wanda ya haura rabin jimillar bashi, yayin da jihohi da Babban Birnin Tarayya suka ɗauki Naira tiriliyan 4.36.

Bashin waje

Bashin waje ya tsaya a Naira tiriliyan 74.43 a Disamba, 2025, wanda ya kai kashi 46.73 cikin ɗari na jimillar bashi.

  • Ya ƙaru da Naira tiriliyan 4.14 daga Naira tiriliyan 70.29 a Disamba, 2024.
  • A cikin kwata, ya ƙaru da Naira tiriliyan 2.95 daga Naira tiriliyan 71.48 a Satumba, 2025.
  • A ma’aunin dala, bashin waje ya ƙaru daga dala biliyan 45.78 a Disamba, 2024 zuwa dala biliyan 51.86 a Disamba, 2025.

Gwamnatin Tarayya ta ɗauki Naira tiriliyan 66.27 na bashin waje, yayin da jihohi da FCT suka ɗauki Naira tiriliyan 8.16.

Tsarin bashi

Duk da ƙaruwar, tsarin bashi ya ci gaba da kasancewa mai daidaito, inda aka fi karkata ga bashin cikin gida.

  • Bashin cikin gida ya kai kashi 53.27 cikin ɗari a Disamba, 2025, idan aka kwatanta da kashi 51.41 cikin ɗari a Disamba, 2024.
  • Bashin waje ya sauka daga kashi 48.59 cikin ɗari zuwa kashi 46.73 cikin ɗari a wannan lokaci.

DMO ta bayyana cewa alkaluman Disamba, 2025 na wucin gadi ne, kuma an yi amfani da farashin musayar Dala na Babban Bankin Najeriya (CBN) na N1,435.2571/$ wajen lissafi.