Ana binciken likitoci kan mutuwar Maradona

Za a ci gaba da binciken likitocin har zuwa karshen watan Yuli.

Ana binciken likitoci kan mutuwar Maradona

A yanzu bayan watanni bakwai da mutuwar fitaccen dan kwallon Argentina, Diego Armando Maradona, ana ci gaba da binciken likitocin da suka yi jinyarsa kan mutuwarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, masu gabatar da kara sun fara neman amsar tambayoyi a wurin tawagar likitoci ta mutum bakwai da suka kula da lafiyarsa gabanin mutuwarsa.

Bayanai sun ce kwamitin kwararru da ke bincike kan mutuwar Maradona na son tabbatar da zargin samun tangarda ko sakaci wajen kula da lafiyar fitaccen dan kwallon.

Ana sa ran ci gaba da binciken likitocin har zuwa karshen watan Yuli.

Wasu dai na zargin cewa Maradona bai samu kulawar da ta dace ba wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.

Daga cikin wadanda ake yi wa tambayoyi akwai likitan da ya yi wa dan kwallon tiyata da kuma likitansa, sai kuma wasu ma’aikatan jinya guda uku.

Aminiya ta ruwaito cewa, a watan Nuwamban bara ce Maradona ya mutu sakamakon bugun zuciya, makonni bayan an yi masa tiyatar a daskarewar jini a kwakwalwa.

Marigayin ya yi rayuwa ta shahara mai cike da kwan-gaba-kwan-baya da cece-kuce, musamman ganin yadda ta’ammali da hodar iblis da barasa fiye da kima ya yi tasiri a lafiyar dan wasan mai matukar kuzari da basira a harkar taka leda.