Ana binciken mutum hudu game da kwakule idon yaro a Zariya
Sakamakon tashi tsaye da jama’ar unguwanin Jushi da Banzazzau Tsohuwa da Sabuwa da ke Zariya a Jihar Kaduna suke yi wajen kula da unguwanninsu ta bangagare tsaro baya da matsafa suka addabi unguwanin da cire sassan jikin mutane an kama wadansu da ake zargi suna da hannu a kwakule idon yaron nan dan shekara hudu […]

Sakamakon tashi tsaye da jama’ar unguwanin Jushi da Banzazzau Tsohuwa da Sabuwa da ke Zariya a Jihar Kaduna suke yi wajen kula da unguwanninsu ta bangagare tsaro baya da matsafa suka addabi unguwanin da cire sassan jikin mutane an kama wadansu da ake zargi suna da hannu a kwakule idon yaron nan dan shekara hudu a Zariya.
A ranar Juma’a da ta gabata da misalin karfe 12:30 na rana mutanen Unguwar Banzazzau Tsohuwa suka kama wani wanda suka yi wa zaton yana daga cikin masu aikata irin wadannan munanan barna, a unguwar wadda titi ne ya raba ta da unguwar da aka kwakule idon Abubakar Sadik makon shida da suka wuce.
Bayan haka a ranar Talata makon jiya an sake yunkuri kwakule wa wani yaro mai suna Ibrahim Mannir dan shekara biyu da suke zaune a Banzazzau Sabuwa ido, wanda hakan ya sa mutanen da suke da makwabtaka da juna suka rude kuma suke kaffa -kaffa da duk wanda ba su amince da shi ba.
Aminiya ta ziyarci unguwanin inda mahaifiyar Ibrahim Mannir yaro na biyu da aka yi yunkurin kwakule masa ido, mai suna Zulaihatu Yusuf ta shaida mata cewa, “A ranar Talata da misalin karfe 11:00 na rana, na shiga gidan yayar maigidana da ke kusa da mu, muna gaisawa da ita sai dana Ibrahim ya biyo ’ya’yanta waje, ko minti biyu ba a yi ba suka shigo ba shi, na ce ina yake suka ce ba su gan shi ba, sai muka fito muka bazama nema muna cikin duddubawa sai muka ji kuka a cikin kango muna shiga sai muka ga yaro an daure kafafuwa da hannayensa, amma ba mu tarar da kowa a wurin ba. Sai muka sanar da mai unguwa yana zuwa ya sa aka kwance yaron aka fara duba wuraren koda za a ga wanda ba a amince da shi ba kuma mai unguwa ya kira ’yan sanda ya sanar da su.
Mai unguwar Banzazzau, Malam Hassan Dabo ya ce, yana isowa ya samu yaron a daure sai ya kwance shi saboda yana da alaka da sashin lafiya sai da ya duba jinkinsa ko zai ga wani lahani ko rauni. Da ya ga babu abin da ya same shi kuma babu wata allura da wadanda suka daure shi suka yi masa, don haka bayan ya shaida wa hakiminsa sai suka dunguma ofishin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda tare da ’yan sanadan da aka turo domin su dauki bayanin abin da ya faru.
Ya ce “Ana cikin haka ne sai rububin kama Muhammad Shehu wanda ’yan unguwar suke zargin yana daya daga cikin masu aikata wannan danyen aiki na hallaka yara ana raba su da sassan jikinsu ta taso.”
Mai unguwar Tsohuwar Banzazzau, Alhaji Salisu Ibrahim Banzazzau ya ce a ranar Juma’a gab da fara tafiya masallaci sai aka sanar da shi cewa ga wani a zaune a dakali wanda ba a amince da shi ba, “Ni kuma nan take na tura samarin gidana, amma saboda larurar rashin lafiya dana zai yi muku bayanin abin da ya faru,” inji shi.
dan mai unguwar mai suna Sama’ila ya shaida wa wakilinmu cewa, “Mun isa wajen tare da ’yan uwana muka samu wanda ake zargin zaune a dakali amma ba mu same shi da komai da za a ce zai iya cutarwa ba. Mun fara yi masa tambayoyi sai jama’a suka kewaye mu suka fara iface-iface suna cewa a kona shi ko a kashe shi. Suka fara jifa tare da duka, sai wata makwabciyarmu da aure ya kawo ta unguwar ta fito tana ihu tana cewa ta san shi ba ya da hankali mu kuma muna ta kokarin kare shi. Haka dai aka yi ta yi har muka yi nasarar ceto shi daga nan muka dunguma zuwa ofishin ’yan sanda daga baya muka gane cewa dan Bayan Silima ne da ke Tudun Wada kuma tabbas ba ya da hankali.
Da wakilinmu ya je unguwar su Muhammad Shehu wanda ke zaune a gida mai Lamba 66, Bayan Albarka Silima a Tudun Wada, Zariya, ya tarar da iyalai da makwabtan wanda ake zargin suna shawarwarin yadda za su fuskanci hukuma su tabbatar mata cewa dansu mahaukaci ne.
Jagoransu kuma Limamin Juma’a na Bakin Kasuwar Tudun Wada, Malam Muhammadu Auwal, ya ce Muhammad Shehu da ne a wurinmu domin ni ne na karba wa mahaifin aure mahaifiyarsa, kuma a yanzu haka ma maraya ne domin iyayensa duk sun rasu. Ya samu larurar tabin hankali sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsa shekara takwas da suka wuce, kuma ba ya rikici da kowa. Idan haukarsa ta sauka yakan yi sana’arsa ta kafinta. Mahaifinsa, wanda ya rasu shekara biyu da suka wuce yana kai shi asibitin mahaukata amma tunda ya rasu ba a sake kai shi ba, don haka muke kokarin tattara shaidunmu da suke nuna cewa yaron nan mara lafiya ne.
A ofihsin Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Mai kula da Shiyya ta daya AC Muhammadu Shehu ya ce tabbas sun fara kama wasu daga cikin wadanda ake zargi suna da alaka da wannan ta’addanci sun kama daya a Sabon Garin Zariya ga kuma wannan.
Game da tabin hankalin da aka cewa mutum na biyu yana da da shi kuwa, sai ya ce sun ce a gabatar da wata shaida da za ta nuna cewa yana da lalurar tabin hankalin. Ya ce, “A tattaunawar da muka yi da shi bai nuna mana wata alamar ba ya da lafiya ba, kuma ka san yawanci wadanda ke sa su sune suke hikima ko suke koya musu cewa idan an kama su to su nuna cewa su mahaukata ne, don haka muke bukatar shaidar da za ta nuna cewa mahaukaci ne sai mu sake shi. Yanzu haka muna tattara bayananmu za mu tura su ofishinmu da ke Kaduna, domin ci gaba da bincike.”
Wani dan sanda ta bayan fage ya shaida mana cewa sun kai samame unguwar a ranar Litinin sun kara kama mutum biyu da suke zargi da irin wannan mugun hali.