Ana binciken sojojin da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai Mali
Baya ga kashe ministan tsaron Mali, sun ƙwace sansanonin sojoji da garuruwa a Arewacin ƙasar.
A ƙasar Mali, yayin da ake ci gaba da zaman dar-dar, hukumomin ƙasar sun sanar da ƙaddamar da bincike biyo bayan hare-haren da ’yan bindiga da ke da alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda da ’yan tawayen Abzinawa ’yan aware suka kai a wasu biranen ƙasar kama daga Bamako zuwa Sevare, Kati, Kidal a ranar 25 ga Afrilu.
Waɗannan hare-hare na daɗa nuni ta yadda majalisar sojin ta Mali ta yi rauni, ganin yadda maharan suka shirya da kuma yawo daga wani yankin zuwa wani wurin daban ba tare da sun fuskanci barazana ba, wanda ya kuma kai ga kashe ministan tsaron Mali.
Babban mai shiga da kara, ya umurci a gudanar da bincike inda ake kyautata zaton maharan sun samu goyon baya daga cikin gida.
Yanzu haka duk da waɗannan matakai da hukumomin sojin na Mali suka sanar da dauka, bai hana ’ƴan tawayen ci gaba da nuna bidiyo na nasarorin da suka samu ba.
Baya ga kashe ministan tsaron Mali, sun ƙwace sansanonin sojoji da garuruwa a Arewacin ƙasar.
Mutanen da aka kama yanzu haka sun haɗa da sojoji uku masu aiki, wani soja mai ritaya da wani soja wanda aka “kora” kuma aka kashe a faɗa kusa da babban sansanin sojojin ƙasar da ke Kati, mai nisan kilomita 15 daga babban birnin Bamako, in ji sanarwar da mai gabatar da ƙara a kotun soji da ke Bamako, wacce aka karanta a talabijin na kasar a daren Juma’a.
“An yi nasarar kama waɗanda suka aikata laifin, kuma ana ci gaba da neman wadanda suka aikata laifin, da waɗanda suka taimaka wa ’yan ta’adda,” in ji sanarwar, ba tare da bayyana adadin waɗanda ake zargi da kuma waɗanda aka kama musamman ba.