Ana bugar da ’yan kunar bakin waken Boko Haram da kwaya – UNODC
Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Majalisar dinkin Duniya (UNODC), ta ce ana samun kwayar taramadol (taramol) a cikin aljifan wadanda suke son kai hare-haren kurnar bakin wake a wuraren da ake aikata ta’addanci. Hukumar ta ce yawan kwayar da aka kwace daga shekarar 2013 ya karu matuka daga kilo 300 zuwa fiye da […]

Hukumar Yaki da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Majalisar dinkin Duniya (UNODC), ta ce ana samun kwayar taramadol (taramol) a cikin aljifan wadanda suke son kai hare-haren kurnar bakin wake a wuraren da ake aikata ta’addanci.
Hukumar ta ce yawan kwayar da aka kwace daga shekarar 2013 ya karu matuka daga kilo 300 zuwa fiye da tan uku a kowace shekara.
Gidan rediyon BBC da ya ruwaito labarin ya ce, hukumar ta ce an gano kwayoyi miliyan uku a wasu akwatuna masu tambarin Majalisar dinkin Duniya a Jamhuriyar Nijar a watan Satumban da ya gabata.
Kuma ta ce mayakan kungiyar Boko Haram na amfani da kwayar ta tramadol.
kwayar da ake amfani da ita domin rage zafin ciwo, ana tsamanin cewa ana amfani da ita ce wajen bugar da hankalin wadanda za su kai hari, kuma Jaridar Guardian a baya-baya nan ta wallafa rahoton da ya ce mayakan Boko Haram kan zuba kwayar cikin dabinon da suke ba yara kafin su tura su su kai hari.
A watan Augustan da ya gabata ne aka kwace kwayar tramadol dubu 600 da za a kai wa kungiyar Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Kamaru.
Wakilin Hukumar UNODC a Afirka ta Yamma, Pierre Lapakue, ya yi gargadin cewa bai kamata a bar yanayin da ake ciki ya ci gaba da gudana ba, saboda hakan zai yi kafar ungulu ga tsaron duniya.
“Ana ganin kwayar tramadol a cikin aljifan mutanen da aka kama, wadanda ake zargin ’yan ta’adda ne a yankin Sahel ko wadanda suka kai harin kurnar bakin wake,” inji Mista Lapakue
“Wannan ya sa alamar tambaya game da wadanda suke samar da wadannan kwayoyi ga mayakan Boko Haram da kuma al-kaeda, ciki har da yara maza da mata wadanda suke shirin kai harin kurnar bakin wake.”
Hukumar ta UNODC ta ce kwayar wadda miyagun kungiyoyi suke safararta daga Asiya da kasashen Larabawa ta koma wata babbar matsala a tsarin kiwon lafiyar yankin Sahel, musamman a Arewacin Mali da Nijar, inda yawan matasan da ke kasashen da ke Kudu da Sahara masu safarar miyagun kwayoyi ke samun kasuwa.
Wata mace a Mali ta fada wa hukumar cewa takan ga yara masu shekara 10 suna tafiya bayan an ba su kwayar a cikin shayi domin su daina jin yunwa.
Hukumar ta UNODC ta ce mutanen da ke shan kwayar ta haramtaciyyar hanya na shan ta fiye da kima, abin da ya zarta adadin da likitoci suke ba da wa ga marasa lafiya har sau biyar.