Ana bukatar Dala miliyan 78 don kula da ’yan gudun hijira

Albarkacin zagayowar ranar bikin tunawa da ’yan gudun hijira a farkon wannan makon, babban jami’in da ke kula da ’yan gudun hijira a kasar Kamaru Khassim Diagne ya bayyana cewa suna bukatar Dala miliyan 78 kula da ’yan gudun hijira dubu 300 wadanda akasarinsu ’yan asalin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ne da kuma Najeriya.Baya ga wadannan […]

Ana bukatar Dala miliyan 78 don kula da ’yan gudun hijira
Ana bukatar Dala miliyan 78 don kula da ’yan gudun hijira

Albarkacin zagayowar ranar bikin tunawa da ’yan gudun hijira a farkon wannan makon, babban jami’in da ke kula da ’yan gudun hijira a kasar Kamaru Khassim Diagne ya bayyana cewa suna bukatar Dala miliyan 78 kula da ’yan gudun hijira dubu 300 wadanda akasarinsu ’yan asalin Jamhuriyar Tsakiyar Afirka ne da kuma Najeriya.
Baya ga wadannan kuma babban jami’in ya ce akwai wasu mutane dubu  200 ’yan asalin Kamaru wadanda suka kaurace daga matsuguninsu domin neman kubutar da rayukansu sakamakon rikicin da kungiyar Boko Haram da kuma ambaliyar ruwa.
Dangane da haka gwamnati ta kafa wani kwamiti na hadin gwiwa tsakanin ma’aikatun harkokin waje da kuma ta cikin gida domin su samu hanyoyin da za su  sa wadannan ’yan gudun hijira rayuwa a cikin tsaro da kuma samar musu wasu ababan more rayuwa.
Har ila yau, kwamitin ya samu raba kyautar kayayyakin mararufi na Dala miliyan biyu da Shugaban kasa Paul Biya ya tallafa wa ’yan gudun hijira da su.
A bara kwamitin ya yi aiki a kan wasu shirye-shirye kamar samar da ruwan sha a sansanin ’yan gudun hijira a Minawao.
Sai dai duk da haka akwai sauran manyan bukatun ’yan gudun hijiran da ba a sauke musu ba. Bayan sanya hannu da hukumomin Kamaru da Najeriya tare da Hukumar Kula da ’yan Gudun Hijira suka yi a ranar 9 ga wannan watan a birnin Abuja game da mayar da ’yan gudun hijiran Najeriya gida. Ana jiran kammala wannan tsarin zuwa nan da karshen watan gobe.