Ana ci gaba da aikin ceto mahaka ma’adinai a Indiya
Ma’aikata masu ayyukan ceto a Jihar Meghalaya da ke Arewa maso Gabashin Indiya sun ci gaba da kwashe ruwa da manyan injuna a kokarinsu na ceto wadansu masu hakar ma’adinai bayan ambaliyar ruwa ta cika ramin da suke hako ma’adinan. Ma’aikatan ceto sun shafe kwanaki suna kwashe ruwan daga ramin da masu hako ma’adinan ke […]
Masu aikin ceto
Ma’aikata masu ayyukan ceto a Jihar Meghalaya da ke Arewa maso Gabashin Indiya sun ci gaba da kwashe ruwa da manyan injuna a kokarinsu na ceto wadansu masu hakar ma’adinai bayan ambaliyar ruwa ta cika ramin da suke hako ma’adinan.
Ma’aikatan ceto sun shafe kwanaki suna kwashe ruwan daga ramin da masu hako ma’adinan ke ciki kafin lokaci ya kure musu a wannan yanki mai nisa na jihar Meghalaya.
A yanzu sun fara amfani da manyan injuna wajen zuke ruwa da aka kawo daga wasu sassan kasar. Kuma sojojin ruwan Indiya na amfani da wani karamin jirgin ruwa mai nutsewa cikin ruwa a kokarin ceto mutanen.
Babu halin aikawa da masu ceton cikin ramin sai an kwashe yawancin ruwan da ke ciki, kuma babu wanda ya san ko mutanen da ruwan ya rutsa da suna da rai zuwa yanzu.
Saheb Ali na daya daga cikin masu hako ma’adinan da ya tsallake rijiya da baya lokacin da ambaliyar ta rutsa da su, ya bayyana wa BBC yadda abin da faru cewa, “Lokacin da na isa can cikin ramin da muke hako ma’adinan, kuma na sauke dutse, sai na ji wata iska mai sanyi. Sai na kara shiga ciki amma jim kadan sai na ga ruwa mai karfi na kwarara cikin ramin. Akwai mutane a ciki kuma suna ta kururuwa amma babu wanda ya ji ni.”
Iyalan mutanen da ruwan ya rutsa da su a ramin sun yi dafifi a kusa da wurin, kuma sun roki jami’ai masu aikin ceton su nemo musu ’yan uwansu.
Irin wadannan wuraren da ake hako ma’adinai da aka lakaba wa sunan ramukan bera na da yawa a Meghalaya. Wannan lamari shi ne na baya-bayan nan, kuma gwamnatin jihar ta dade tana kokarin rufe su musamman a shekaru biyar da suka gabata.