Ana ci gaba da alhinin rashin masoyin Buhari a Bauchi

Sakamakon rashin daya daga cikin masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma fitaccen dakarensa, Alhaji Abdulwahab Gambo da ake kira da Baba Mai Alkalami ko Baba Mai Masara da babur ya kade shi  a Titin kofar Ran da ke cikin garin Bauchi, jama’a na ci gaba da alhinin rasuwarsa. Dattijon mai shekara 62, ya rasu ya […]

Ana ci gaba da alhinin rashin masoyin Buhari a Bauchi
Ana ci gaba da alhinin rashin masoyin Buhari a Bauchi

Sakamakon rashin daya daga cikin masoya Shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma fitaccen dakarensa, Alhaji Abdulwahab Gambo da ake kira da Baba Mai Alkalami ko Baba Mai Masara da babur ya kade shi  a Titin kofar Ran da ke cikin garin Bauchi, jama’a na ci gaba da alhinin rasuwarsa.

Dattijon mai shekara 62, ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya 11da mahaifiyarsa wacce ta haura shekara 100. 

Rasuwarsa tana ci gaba da jan hankali al’ummar jihar da kasa baki daya.

dan uwan mamacin, mai suna Magayaki ya ce alakar marigayin da Buhari kauna ce ta siyasa da ta shiga tsakaninsu tun shekarar 2003 lokacin da Buhari ya fara fitowa takara. “Wannan kauna ta yi karfi har ta kai matsayin da kafin Buhari ya zama Shugaban kasa duk lokacin da yake so ya gan shi Buhari yakan ba shi lokaci su gana,” inji shi.

Ya ce amma bayan Buhari ya zama Shugaban kasa Allah bai sa ganawa ta yawaita a tsakaninsu ba, saboda wadansu mukarraban Shugaban sun kange shi. “An taba ba shi gayyata har ya shiga fadar Shugaban kasa aka yi Sallar Juma’a da shi, amma Allah bai sa da shi da masoyinsa ba. A Babbar Sallar Idin da ya wuce ma ya je har Daura har Shugaban kasa ya daga masa hannu, amma duk kokarin da wadansu daga cikin makusatan Shugaban suka yi don su sada su Allah bai nufi ganawarsu ba,” inji shi.

Ya ce kafin Shugaba Buhari ya zama Shugaban kasa saboda karfin zumunci sau biyu yana zuwa gaisuwar ta’aziyya kan rashe- rashen da aka yi wa Baba Mai Alkalami, kuma sau biyu Buhari na zuwa ya gana da mahaifiyar marigayin a Bauchi. “Ko lokacin da ya yi rashin lafiya aka yi yunkurin kashe shi har ya yi ta zubar da jini a Kano, Buhari ya je ya gaishe shi a asibiti, kuma ya sake komawa ya samu an sallame shi,” inji Magayaki.

Ya ci gaba da cewa, Baba Mai Alkalami kullum damuwarsa damuwar al’umma ce, “A ganinsa bai kamata dan Adam ya shiga kunci da damuwa ba, kuma mutum ne mai son alheri da taimako a duk lokacin da ya ga mutum a cikin matsala. Kuma duk da cewa ya yi karatu da yawa yana da digiri har hudu, ya kuma yi aiki a Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Bauchi, amma har ya rasu bai mallaki gidan kansa ba. Al’umma na jimamin rashinsa saboda saukin halinsa da karamcinsa,” inji shi.

 

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa