Ana ci gaba da binciken dalilin nutsewar jirgin Koriya
Hukumomi a kasar Koriya ta Kudu suna ci gaba da binciken dalilin hadarin jirgin ruwan kasar wanda ya nutse a makon da ya wuce, a dai-dai lokacin da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura dari. Adadin fasinjojin da suka rasu ya karu ne bayan da masu aikin ceto suka gano karin wasu gawawwaki […]

Hukumomi a kasar Koriya ta Kudu suna ci gaba da binciken dalilin hadarin jirgin ruwan kasar wanda ya nutse a makon da ya wuce, a dai-dai lokacin da adadin mutanen da suka rasa rayukansu ya haura dari.
Adadin fasinjojin da suka rasu ya karu ne bayan da masu aikin ceto suka gano karin wasu gawawwaki daga cikin jirgin. Sai dai har yanzu ba a tsaya da aikin ceton ba, saboda akwai sauran fasinjoji 181 da ba a ji duriyarsu ba. Jami’an tsaro dai sun cafke direban jirgin da kuma ma’aikatan jirgin bakwai don su ba da ba’asin yadda hadarin ya faru.
Yawancin fasinjojin jirgin dai dalibai ne ‘yan makaranta wanda ke hanyarsu ta zuwa yawon-bude-ido tsibirin Jeju. Wani wanda ke aikin ceto ya shaida wa kafar yada labarai ta CNN cewa “yanayin mummuna ne, muna ci gaba da aikin ne da fatan ko za mu gano wasu da rai. Amma duk lokacin da muka iso inda iyalen fasinjojin suke ba tare da ceto wasu da ke da sauran numfashi ba, mu kan kasa fuskantarsu saboda irin girman damuwar da suke ciki”. Inji shi
Wani jami’in ya ce sakamakon wani kwarya-kwaryar bincike da aka gudanar, an tuhumi direban jirgin da kuma biyu daga cikin ma’aikatan jirgin da laifin sakaci da kuma fita daga jirgin kafin kammala aikin ceton fasinjoji.
Shugabar kasar Park Geun-hye ta bayyana su da wadanda suka aikata kisan kai dalili da yin sakaci da aiki kuma kasar ba za ta taba yafe masu ba. Sai dai ba duka ma’aikatan jirgin ba ne ake tuhuma haka, saboda akwai wadanda aka ruwaito sun taimaka wa fasinjojin inda har wasu daga cikinsu suma suka rasa rayukansu.Wata jaridar kasar mai suna Korea Herald, ta ce direban ka iya fuskantar hukuncin daurin rai-da-rai idan kotu ta same shi da laifi.