Ana ci gaba da ceto fasinjojin jirgin ruwan Koriya ta Kudu
Masu gadin teku a kasar Koriya ta Kudu na ci gaba da aikin ceto domin gano fasinjoji kusan 300 da ba a gansu ba, bayan wani jirgin ruwan fito ya nutse a kudancin gabar ruwan kasar.Jirgin ruwan mai suna Sewol yana dauke ne da fasinjoji 475 wanda ciki har da ’yan makaranta, wadanda aka ceto […]

Masu gadin teku a kasar Koriya ta Kudu na ci gaba da aikin ceto domin gano fasinjoji kusan 300 da ba a gansu ba, bayan wani jirgin ruwan fito ya nutse a kudancin gabar ruwan kasar.
Jirgin ruwan mai suna Sewol yana dauke ne da fasinjoji 475 wanda ciki har da ’yan makaranta, wadanda aka ceto su jim kadan bayan nutsewarsa a safiyar shekaranjiya Laraba, yayin da aka tabbatar da mutuwar fasinjoji biyu. Hukumonin Koriya ta Kudu dai sun ce jirgin wanda kuma yake dauke da motoci 150 ya fara samun tangarda ne a lokacin da ya nausa tsibirin Jeju.
Aikin ceton dai na samun taimako daga sojan ruwan Amurka inda suka isa tekun da jiragen ruwa masu yawa da kuma kananan jiragen sama, masu saukar ungulu. Zuwa lokacin rubuta rahoton, ba a iya gano musabbabin nutsewarsa ba, amma wani da al’amarin ya faru a idonsa ya shaida wa gidan talabijin din YTN cewa ya ji wata kara jim kadan kafin nutsewar jirgin.
Jirgin dai ya tashi ne daga gabar ruwan Incheon, wacce ke da nisan kilomita 30 yamma da babban birnin kasar Seoul da maraicen ranar Lahadi.