Ana ci gaba da gaisuwar ta’aziyyar Katukan Misau
Iyalan fitaccen dan siyasar nan a Jihar Bauchi, Alhaji Babayo Ahmad, Katukan Misau suna ci gaba da amsar gaisuwa, bayan rasuwarsa a ranar Larabar makon jiya. Katukan Misau ya rasu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Bauchi zuwa Maiduguri a kusa da garin Soro, lokacin da daya daga cikin ’ya’yansa […]

Iyalan fitaccen dan siyasar nan a Jihar Bauchi, Alhaji Babayo Ahmad, Katukan Misau suna ci gaba da amsar gaisuwa, bayan rasuwarsa a ranar Larabar makon jiya.
Katukan Misau ya rasu ne sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Bauchi zuwa Maiduguri a kusa da garin Soro, lokacin da daya daga cikin ’ya’yansa ke tuka shi a mota don zuwa gaisuwar ta’aziya. dan da wani abokin tafiyarsu sun samu raunuka kuma suna jinya a halin yanzu.
Marigayi Katukan Misau, kafin rasuwarsa ya rike mukamai daban-daban a Gwamnatin Ahmadu Mu’azu, kuma, wakili ne a kwamitin da Gwamnatin Jihar Bauchi ta kafa domin sake duba sauke masarautun gargajiya da gwamnayin ta yi.
Ya rasu yana da shekara 78 a duniya, ya bar matan aure uku da ’ya’ya 22. Kuma an yi Sallar jana’izarsa a kofar fadar Mai martaba Sarkin Bauchi.
Shugaban Sashen Ayyuka na Hukumar Kiyaye Hadurra ta kasa da ke Jihar Bauchi, Mista Paul Gua ya tabbatar da aukuwar hadarin. Ya ce tayar motarsu kirar Fijo 406 mai lamba FKJ 918Cb ta fashe lamarin da ya jawo hadarin.