Ana ci gaba da gwabza fada a Ukraine duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Ana ci gaba da gabza fada tsakanin sojojin kasar Ukraine da ’yan tawayen kasar wadanda suke samun goyon baya daga kasar Rasha duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarori biyun suka cimma. Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce tuni sojojin kasar suka fara kwashe kayansu daga yankin Debaltsebe bayan cimma yarjejeniyar.Poroshenko a shekaranjiya Laraba […]

Ana ci gaba da gwabza fada a Ukraine duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Ana ci gaba da gwabza fada a Ukraine duk da yarjejeniyar tsagaita wuta

Ana ci gaba da gabza fada tsakanin sojojin kasar Ukraine da ’yan tawayen kasar wadanda suke samun goyon baya daga kasar Rasha duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarori biyun suka cimma.

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya ce tuni sojojin kasar suka fara kwashe kayansu daga yankin Debaltsebe bayan cimma yarjejeniyar.
Poroshenko a shekaranjiya Laraba ya ce fiye da kashi 80 cikin 100 na sojojin kasar suka janye, sannan sauran kashi 20 din ma za su janye a hankali.
Debaltsebe, yanki ne da dukkan bangarorin suke son kabar iko da shi saboda muhimmancinsa.
“Sojojin kasar Ukraine da sauran jami’an tsaro sun kammala dukkan shirye-shiryen barin Debalsebe.” Inji Poroshenko cikin wani ‘sako mai murya’ da mai magana da yawunsa ya fitar.
Idan ba a manta ba dai a makon jiya ne aka cimma yarjejeniyar tsagaita wutar a Belarus da ke kasar Belgiyum, inda kasashen da suka zauna a teburin sulhun suka hada da Ukraine da Rasha da Jamus da kuma Faransa.
Sai dai a yarjejeniyar, ba a ambaci Debaltsebe da ke gabashin Ukraine ba, yankin da ya hada birnin Donesk da Luhansk.
“Wannan al’amarin da yake faruwa bai yi dadi ba. Al’amari ne da ya nuna rashin girmama yarjejeniya.” Inji Federica Mogherini, daya daga cikin wadanda suka shiga tsakani har aka cimma yarjejeniyar.
A ranar Talata shugaban kasar Rasha bladimir Putin ya bukaci sojojin Ukraine su yi saranda.
A ranar Litinin majalisar dinkin duniya ta bayyana an kashe mutane 5, 000, sannan miliyan 1 sun yi gudun hijira sakamakon rikicin kasar Ukraine.