Ana ci gaba da neman Jirgin saman Malaysia da ya bace
Hukumar da ke lura da sararin samaniya ta duniya ta shiga sahun masu neman jirgin saman Malaysia nan da ya bace ranar Asabar da ta gabata. Hukumar za ta hada hannu ne da jiragen ruwa 42 da na sama 39 a aikin neman jirgin da ba a taba yin irinsa ba a tarihi. Za ta […]
Hukumar da ke lura da sararin samaniya ta duniya ta shiga sahun masu neman jirgin saman Malaysia nan da ya bace ranar Asabar da ta gabata.
Hukumar za ta hada hannu ne da jiragen ruwa 42 da na sama 39 a aikin neman jirgin da ba a taba yin irinsa ba a tarihi. Za ta yi amfani ne da tauraron dan Adam domin gano jirgin.
Ana dai amfani da hotunan da tauraron dan Adam ya dauka ne don samun gamsasshun bayanai abubuwan da suka faru jim kadan kafin faruwar hadarin da kuma bayan faruwarsa.
Jirgin dai ya tashi ne daga babban birnin Malaysia wato Kuala Lumpur zuwa garin Beijing na kasar China a safiyar ranar Asabar da ta gabata. An dai yi magana da shi ta karshe ne sanda ya lula kilomita dubu 10 da 600 daga kasa, a tsakanin kasar Malaysia da kudancin kasar bietnam daga nan ne ba a kara jin duriyarsa ba.
Ministan Sufurin Malaysia ya bayyana cewa an kara fadin inda ake neman jirgin. Ya shawarci iyalan wadanda ke cikin jirgin su kwantar da hankulansu. Yana mai bayar da tabbacin cewa hukumomin kasar ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun gano jirgin. kasashe 12 ne ke aikin neman jirgin zuwa yanzu.