Ana ci gaba da neman yaran da ruwan sama ya tafi da su
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) na ci gaba da aikin nemo yaran da ruwan sama ya tafi da su a jihar. Jami’an hukumar LASEMA sun ce sun fara aikin neman daukacin yara har ma da manya da ambaliyar ta tafi da su, ta hanyar binciken manyan magudanan ruwa daga yankin Surulere, […]
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA) na ci gaba da aikin nemo yaran da ruwan sama ya tafi da su a jihar.
Jami’an hukumar LASEMA sun ce sun fara aikin neman daukacin yara har ma da manya da ambaliyar ta tafi da su, ta hanyar binciken manyan magudanan ruwa daga yankin Surulere, inda za a fadada zuwa sauran manyan magudanan ruwa a fadin jihar.
Jami’an sun fara aikin ne bayan samun rahoto cewa ruwa ya tafi da wata budurwa ‘yar shekara 17 mai suna Aishat bayan an dauke ruwan sama a ranar Litinin, 22 ga watan Yuni.
Wannan na zuwa ne bayan ruwan saman ya tafi da wata yarinya ‘yar shekara hudu a yankin Agege a makon jiya.
- Ambaliyar ruwa ta raba mutum 300 da gidajensu
- Iska mai karfi ta rusa gidaje 300 a Kebbi
- Mutane sun mutu, gidaje 600 sun rushe bayan iska mai karfi a Kano
Shugaban LASEMA, Dokta Olufemi Oke-Osanyintolu ya ce budurwar ta bace ne a ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama da aka yi tamkar da bakin kwarya a jihar.
“An sanar mana cewa yarinyar mai suna Aishat ta bata ne a lokacin ambaliyar ruwan a unguwar Alapafuja da ke yankin Surulere a Legas bayan ruwan sama da aka yi kamar da bakin kwarya”, inji shi.
Hukumar ta bukaci iyaye da su rika sanya ido a kan ‘yayansu a lokacin da ake ruwan sama, su kuma hana ‘yayansu fita a irin wannan yanayi, yayin da jami’anta ke ci gaba da aikin neman wadanda ruwan ya tafi da su.