Ana ci gaba da zanga-zanga a Hong Kong

Dubban jama’a masu nuna goyan bayan dimokradiyya suna ci gaba gudanar da zanga-zanga a yankin Hong Kong tsawon mako guda ke nan. Inda cincirundon jama’ar suke rera waken kira ga shugaban yankin da ya yi murabus, wanda a farko ya yi kira ga masu gangamin da su watse.A kalamansa na farko, shugaban kasar China di […]

Ana ci gaba da zanga-zanga a Hong Kong
Ana ci gaba da zanga-zanga a Hong Kong

Dubban jama’a masu nuna goyan bayan dimokradiyya suna ci gaba gudanar da zanga-zanga a yankin Hong Kong tsawon mako guda ke nan. Inda cincirundon jama’ar suke rera waken kira ga shugaban yankin da ya yi murabus, wanda a farko ya yi kira ga masu gangamin da su watse.
A kalamansa na farko, shugaban kasar China di Jinping, bai ce komai game da zanga-zangar ba, abin kawai ya ce shi ne “China za ta kare martaba da ci gaban yankin Hong Kong.”
Kodayake, a shekaranjiya Laraba shugaban daliban yankin  Hong Kong ya ce za su ci gaba da zanga-zangar da kuma mamaye manyan gine-ginen gwamnati, idan har shugabanin yankin suka ki yin murabus.
Shugaban daliban da ke jagorantar masu zanga-zangar Lester Shum, ya ce za su yi maraba da tattaunawa da Gwamnatin China, amma ban da shugabannin yankin . Kodayake galibin masu zanga-zanga suna kira ne ga Gwamnatin China da ta dakatar shirinta na tantance ’yan takarar da za su tsaya takarar zabe a shekarar 2017 a yankin,wanda Birtaniya ta mika wa kasar China a shekarar 1997.