Ana ci gaba da zanga-zanga a Iran
Zuwa yanzu, akalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ke ci gaba da wakana a kasar Iran. Rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar sun ce daga cikin wadanda suka rasu akwai wadansu mutum shida da suka yi nufin shiga wani ofishin ’yan sanda a garin kahdarijan da ke Lardin Isfahan. Hakan kuma […]

Zuwa yanzu, akalla mutum 21 ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar da ke ci gaba da wakana a kasar Iran.
Rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar sun ce daga cikin wadanda suka rasu akwai wadansu mutum shida da suka yi nufin shiga wani ofishin ’yan sanda a garin kahdarijan da ke Lardin Isfahan.
Hakan kuma an kama daruruwan mutane a babban birnin kasar, kamar yadda Mataimakin Gwamnan Tehran, Ali Asghar Naserbakht ya sanar.
Ita dai wannan zanga-zanga, da ta faro daga yammacin birnin Mashhad a makon jiya, ita ce zanga-zanga mafi girma da kasar Iran ta fuskanta tun bayan zanga-zangar da aka taba yi a shekarar 2009 kan zaben kasar.
Wannan karon, ana zanga-zangar ce saboda nuna rashin amincewa da yadda mutanen kasar suka shiga mawuyacin halin matsin tattalin arziki, kuma zanga-zangar ta mamaye sassan kasar.
Yadda lamarin ya samo asali
Siyasar Iran ta kasu kashi biyu ne tun bayan juyin juya-halin kasar a tsakanin masu ra’ayin sauyi da masu ra’ayin rikau. Tsohon Shugaban Kasar Mohammad Khatami ne ke jagorantar masu ra’ayin sauyi da suke fafutikar samar da sauyi a kasar ta hanyar canja yanayin tafiyar da kasar da siyasar kasar. Su kuma bangaren masu ra’ayin rikau sun fi nuna goyon ne ga Ayatollah Ali Khamenei, inda suke ci gaba da fafutikar ganin kasar ta ci gaba da wanzuwa yadda take kamar yadda kafar labarai ta ABC News ta ruwaito.
Shugaban Iran, Hassan Rouhani, yana cikin masu ra’ayin tsaka-tsaki ne, amma ya samu goyon bayan masu ra’ayin sauyi a zaben 2013, inda ya dauki alkawarin kawo sauyi kan yadda ake tafiyar da kasar, da sauya alakar da ke tsakanin kasar da kasashen waje bayan takunkumi da kasar ta rika shiga a lokacin da masu ra’ayin rikau ke mulki. Rouhani ya ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai irin su Amurka da Ingila da Rasha da Faransa da Jamus da sauransu, inda hakan ya yi sanadiyar samun matsaya a tsakaninsu a shekarar 2015, Iran ta amince za ta daga kafa a shirinta na makamashin nukiliya, domin a cire mata wasu daga cikin takunkumin da aka kakaba mata.
Haka kuma, a bara ne Rouhani ya sake lashe zabe a karo na biyu tare da goyon bayan masu ra’ayin rikau din. Sannan ya yi alkawarin gyara tattalin arzikin kasar.
Yadda aka fara wannan zanga-zangar
Wannan zanga-zangar wadda ta fi kamari a sauran larduna fiye da birnin Tehran, ma’aikata ’yan kimanin shekara 25 ne suka fi yawa a ciki, domin su ne tabarbarewar tattalin arzikin ya fi shafa. Zanga-zangar ta fara ce a ranar 28 ga Disamban bara a garin Mashhad, wanda shi ne gari na biyu mafi girma a kasar. An fara zanga-zangar kamar wasa, amma ’yan kwanaki kadan sai ta mamaye kasar. Wadansu na kusa da Shugaba Rouhani suna zargin magoya bayan abokin hamayyarsa Ebrahim Raisi da ke Mashhad da fara zanga-zangar. Masu zanga-zangar suna tafiya ne suna fadin munanan kalamai na batanci ga gwamnati.
Zanga-zangar wadda ta faro kan matsin tattalin arziki, wadansu suna ganin akwai siyasa a lamarinta.
Maganganun da masu zanga-zangar ke yi ya tayar wa masu ra’ayin sauyi hankali, wadanda duk da cewa suna neman sauyi a kasar, ba sa son abin da zai kawo faduwar daular Musulunci ta kasar. Wadansu kuma suna ganin abin da ya sa zanga-zangar ta yi kamari shi ne yadda Shugaba Hassan Rouhani ya fara daukar hanya irin ta masu ra’ayin rikau bayan ya samu nasarar lashe zabensa a karo na biyu, kuma ya gaza wajen kawo sauyin yanayin kasar da ya yi musu alkawari
Mutanen kasar dai sun shiga cikin matsin tattalin arziki, sannan kayan masarufi sun kara tsada da kusan kashi 40. Sannan kasar ta fuskanci barkewar annobar murar kaji wadda hakan ya sa aka kashe kaji kusan miliyan 17. Kashe kajin da aka yi da kuma yanayin kasafin kudin da Rouhani ya shirya, sai farashin kwai ya tashi da kashi 50 zuwa 100 kamar yadda kafar yada labarai ta bod ta ruwaito.
Tsadar ta kwai sai ta zama abin kwatance a kan yadda kasar ke fama da matsin tattalin arziki. Wannan ya sa masu zanga-zangar suka taru a Mashhad suna maganganu kamar: “Ba mu amince da tashin farashi ba,” da “Rouhani ya mutu.”
Farfesa Hussein Banai na Jami’ar Indiana, wanda ya yi karatu a Iran ya shaida wa kafar labarai ta bod cewa: “zanga-zangar ta fara ne saboda farashin kwai. Ko a yarda ko kada a yarda, wannan ne asalin lamarin.”
Mutanen Iran sun gaji da mulkin kama-karya – Shugaba Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya tsoma bankinsa a batun zanga-zangar, inda ya wallafa a shafinsa na twitter cewa an dade ana cutar da mutanen kasar ta hanyar mulkin kama-karya, “Mutanen Iran yanzu sun farka kan yadda ake yi musu mulkin kama-karya. Duk kudin da Shugaba Obama ya yi sakarcin ba su, sun karar da shi ne a ta’adanci da aljifansu. Mutanen kasar suna fama da yunwa da tashin farashin kayan masarufi da take hakkin mutane, Amurka na kallo.”
Trump ya kara da cewa suna tare da masu zanga-zangar, inda ya sake wallafawa a shafinsa na twitter cewa, “Ina matukar girmama mutanen Iran bisa yadda suka fara daukar matakin a kan gwamnatinsu masu yi musu mulki da almundahana da cin hanci. Za mu bayar da duk gudunmawar da ta dace domin tallafawa a lokacin da ya dace.”
Mun shawo kan lamarin – Mataimakin Minsitan Cikin Gidan
Mataimakin Ministan Harkokin Cikin gidan Iran, Hossein Zofaghari ya ce sun shawo kan lamarin, kuma kwanan nan masu zanga-zangar za su daina.
Zolfaghari ya ce mutane suna ba jami’an tsaro hadin kai, kuma ba sa amincewa da masu nufin kawo hargitsi da tayar da zaune-tsaye.”
“Jami’an tsaro da ’yan sanda sun nuna juriya da jajircewa ga masu zangar-zangar matukar ba su barnata kayan hukuma ba, ko kuma su kai musu farmaki. Amma kuma sun yi maganin wadanda suke nufin tayar da zaune-tsaye ta hanyar zanga-zangar,” in ji shi.
Makiyan Iran ne suka shirya zanga-zangar
– Khamenei
Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya zargi makiya Iran da taimakawa wajen zafafa zanga-zangar kamar yadda Reuters ya ruwaito.
“A ’yan kwanakin nan, makiya Iran suna amfani da abubuwa da yawa kamar kudi da makamai da siyasa da bayanan sirri wajen tayar da zaune-tsaye a Jamhuriyyar Musulunci ta Iran,” inji shi.
Bai yi bayanin su wane ne makiyan da yake nufi ba a cikin bayanansa, amma Sakataren Majalisar kolin ta Tsaro ta kasar, Ali Shamkhani ya ce , kasashen Amurka da Ingila da Saudiyya suna da hannu a zanga-zangar.
“kasar Saudiyya za su ji amsar da za mu mayar musu, kuma sun san yadda amsarmu take,” kamar yadda aka jiyo Shamkhani yana shaidawa kafar yada labarai ta Tasnim.