Ana ci gaba da zanga-zanga a Missouri
Ana ci gaba da baza jami’an tsaro a garin Ferguson na jihar Missouri a kasar Amurka, kwana guda bayan da zanga-zanga ta barke kan wanke wani dan sandan farar fata da masu yanke hukunci suka yi, bisa zargin shi da kashe wani matashi bakar fata.Gwamna Jihar Missouri, Jay Nidon ya ce akalla jami’an tsaro 2,200 […]
Ana ci gaba da baza jami’an tsaro a garin Ferguson na jihar Missouri a kasar Amurka, kwana guda bayan da zanga-zanga ta barke kan wanke wani dan sandan farar fata da masu yanke hukunci suka yi, bisa zargin shi da kashe wani matashi bakar fata.
Gwamna Jihar Missouri, Jay Nidon ya ce akalla jami’an tsaro 2,200 aka tura yankin, yayin da magajin Garin na Ferguson James Knowles, ya soki irin jinkirin da ake samu wajen aike wa da jam’ian tsaron.
A ci gaba da zanga zangar, masu boren sun datse wata babbar hanya na dan wani lokaci a tsakiyar birnin St. Louis, yayin da rahotanni ke cewa masu zanga-zangar sun yi wata arangama da jami’an tsaro.
Lauyan da ke kare dangin matashin Michael Brown da dan sandan ya harbe, ya ce ba su yi na’am da matsayar da masu yanke hukunci suka dauka ba, na cewa ba za a tuhumi dan sanda ba. Har ila yau, zanga-zangar ta yadu zuwa biranen Oakland da Califoniya. Sai dai zanga-zangar lumana aka yi a biranen New York da Seattle. dan sandan mai suna, Darren Wilson ya kashe matashin Micheal Brown, dan shekara 18 da haihuwa, a ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata a wani yanayi mai daure kai.