Ana dukan Fulani ana fin su kuka a kasar nan – Bodejo
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah Kautal Hore ta kasa Alhaji Abdullahi Bodejo ya koka kan yadda ake dukan Fulani makiyaya kuma a fi su kuka a sassan kasar nan.Alhaji Abdullahi Bodejo ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Tudun Wada da ke Jihar Nasarawa a makon jiya.Ya ce al’ummar […]
Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah Kautal Hore ta kasa Alhaji Abdullahi Bodejo ya koka kan yadda ake dukan Fulani makiyaya kuma a fi su kuka a sassan kasar nan.
Alhaji Abdullahi Bodejo ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Tudun Wada da ke Jihar Nasarawa a makon jiya.
Ya ce al’ummar Fulani sun zama abin farauta a sassan kasar nan ta yadda kabilu da dama suke fada musu su kashe su kuma su sace dabbobinsu, sannan a rika dawowa ana zargin cewa Fulanin ne suke fada wa kabilun ko jama’ar. “Wannan kamar ana dukanmu ne kuma a dawo a fi mu yin kuka,” inji shi
Sai ya yi kira ga Fulanin da ke fadin kasar nan kan su koma kan kyawawan al’adunsu da suka yi watsi da su, kuma su zauna lafiya da sauran kabilun da suke tare da su a sassan kasar nan.”Rigirgimun da al’ummar Fulani ke fuskanta a kasar nan sun samo asali ne sakamakon yin watsi da kyawawan al’adunsu don haka mu koma kan wadannan kyawawan ala’adu na magabatanmu don mu zauna lafiya da juna da kuma makwabtanmu, kuma mu samu martaba a idon jama’a,” inji shi.
Ya ce Fulani al’umma ne masu kawaici da hakuri da kunya, shi ya sa da wuya a ga Bafulatani yana roko ko maula da makamantansu, amma saboda watsi da irin wadannan kyawawan dabi’u sai ga shi yanzu ana samu Fulani suna aikata wasu miyagun ayyuka da suke zubar musu da mutunci.
Ya nuna bakin ciki cewa duk da cewa ana samun Fulani a ko’ina a duniya amma duk da haka su suka fi samun koma baya, maimakon su yi amfani da wannan cudanya da jama’a wajen inganta makomarsu.
“Wajibi ne mu rika tuna da abin da iyayenmu suka yi na rungumar kyawawan al’adunmu, hakan ya sa suka iya cimma nasarori da dama a lokacinsu. kofata za ta kasance a bude a kowane lokaci ga duk wanda ke da shawara domin ciyar da al’ummar Fulani gaba,” inji shi.